GWAMNATIN ZAMFARA TA BANKAƊO YADDA BELLO MATAWALLE YA KWASHE BILIYOYIN NAIRA DA SUNAN GININ GIDAJEN SAUKAN GWAMNA
- Katsina City News
- 30 Oct, 2023
- 1270
BADAƘALA:
Gwamnatin Jihar Zamfara ta fitar da sabbin shaidu waɗanda suke fallasa yadda tsohon gwamna kuma ƙaramin minista, Bello Matawalle ya rattaba hannu kan fitar biliyoyin kuɗi don aikin gidajen saukan gwamna.
Tsohuwar gwamnatin ta Bello Matawalle ta ƙirƙiri aikin ginawa tare da sayo kayayyaki ga gidajen saukan gwamna a ƙananan hukumomi 14 da ake da su a Zamfara.
Wata takardar sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar jiya lahadi a Gusau, ta bayyana cewa takardun da aka fitar suna cikin jerin salsalar fallasa kan irin ɓarnar da Bello Matawalle ya tafka a lokacin yana gwamna.
Ya ƙara da cewa, Gwamnatin Dauda Lawal ba za ta yi shiru ko kawar da kai kan satar rashin imani da tsohuwar gwamnatin ta aikata ba, musamman inda aka bayar da ayyuka, aka kwashi biliyoyi kuma aka yi watsi da ayyukan.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Ya saɓawa ƙa’idar gudanarwar a tsarin gwamnati mutum ya biya kuɗi ɗari bisa ɗari kan kwangilar da ba a fara aiwatarwa ba. Za ka taras da irin waɗannan kwangiloli ga su nan birjik an sace kuɗaɗen al’umma da sunan yin su. Za mu bibiyi duk waɗanda suka tafka irin wannan sata, domin mu dawowa da al’umma haƙƙinsu.
“Daga cikin irin waɗannan ayyuka da tsohuwar gwamnatin Bello Matawalle ta kwashe kuɗaɗe da sunansu akwai batun ginin gidajen saukan gwamna a ƙananan hukumomi 14 na jihar. Wanda tun kafin ma a fara aikin aka kwashe biliyoyi da sunan kuɗin sayo kayan gidajen.
“Bello Matawalle ya fitar da cikakken kuɗi don biyan mafi yawa daga cikin ‘yan kwangilar. Misali, tura ma kamfanin BES BELMON Nigeria Limited Naira Biliyan 1,966,035,160.00 a ranar 27 ga watan Disambar 2021 domin aikin katangewa, sayo kayayyakin cikin gida, da sanya wutar lantarki ga waɗannan gidajen saukan gwamna guda 14, tun ma kafin a fara aikinsu.
“An biya cikakkun kuɗaɗen aiki ga ‘yan kwangilan da ke aikin gina gidajen na suakan gwamna a ƙananan hukumomin Kauran Namoda, Zurmi, Bakura, Maradun, Bukkuyum, Bungudu, da Gummi, tun kafin a fara aikin.
“A ranar 30 ga watan Afirulun 2020 gwamnan ya rattaba hannu don a fitar da kuɗi naira miliyan 324,410,211.00 ga kamfanin SWAT AGA construction Limited domin a gina gidan saukan gwamna a ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda. An fitar da wannan kuɗin ne daga Ma’aikatar Kananan Hukomomi da Masarautu.
“Hakan kuma a ranar dai 30 ga watan Afirilun 2020 ɗin an sake fitar da miliyan 324,410,211.00 ga kamfanin na SWAT AGA Construction Limited a matsayin kuɗin aikin ginin gidan saukan gwamna a ƙaramar hukumar Zurmi.
“Ƙarin abin haushi, wannan kamfanin na BES BELMON wanda aka biya sama da biliyan ɗaya don sayo kayan gidajen da ba a kammala ginawa ba, shi ne a ranar 30 ga watan Afirilun 2020 aka sake fitar da miliyan 324,410,211.00 don ya gina gidan saukan gwamna a ƙaramar hukumar Maradun.
“Muna so a fahimci irin badaƙalar da kamfanin BES BELMON Nig. Limited ke ciki, musamman tarayyar da ya yi wurin fitar da kuɗaɗe daga baitil malin jihar Zamfara ba tare da ƙa’ida ba. A dai ranar 30 ga watan Afirilun 2020 ne Bello Matawalle ya sake fitar da naira miliyan 324,410,211.00 ga BES BELMON don gina gidan saukan gwamna a ƙaramar hukumar Bukkuyum. Abin tambayan shi ne, wa ke da wannan kamfani na BES BELMON?
“Duk dai a ranar 30 ga watan Afirilun 2020, Bello Matawalle ya sa aka fitar da naira miliyan 324,410,211.00 aka ba BES BELMON a matsayin kuɗin gina gidan saukan gwamna a ƙaramar hukumar Bungudu.
“Gwamnatin Zamfara za ta ci gaba da bankaɗo sama da faɗi da rashin gaskiyan da aka tafka ba don komi ba, sai domin tabbatar da adalci.
“Saboda haka ne ma muke kira ga kamfanin BES BELMON Nigeria Limited da ya gaggauta dawowa da gwamnati Naira Biliyan 1,966,035,160.00 da Bello Mohammed Matawalle ya biya shi ba tare da ƙa’ida ba. Aikin ceto muka zo yi, ba za mu ɗagawa maha’inta ƙafa ba.”