Samar da tsaro: An tura Rundunar 'Yan Sanda "Mobile Police" daga jihar Legas a karamar hukumar Kurfi
- Katsina City News
- 16 Oct, 2023
- 936
Katsina Times
A ranar Litinin 16 ga watan Oktoba, 2023 shugaban karamar hukumar Kurfi Hon. Mannir Shehu Wurma ya karbi tawagar 'Yan Sanda Kwantar da Tarzoma Mobile Police daga jihar Legas da aka turo karamar hukumar dangane da kokarin gwamnatin jihar Katsina na magance matsalar rashin tsaro a jihar.
A jawabinsa na maraba, shugaban karamar hukumar ya yiwa jami’an ‘yan sandan Najeriya jawabi a ofishin ‘yan sanda na Kurfi inda ya shawarce su da su ci gaba da gudanar da ayyukan su ba tare da tsoro ko son rai ba, yace hakan shi ne zai sanya a samu kyakkyawar sakamako.
Haka zalika Hon. Mannir Shehu ya yaba wa kokarin Gwamnan Jihar Malam Dikko Umar Radda, wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Kurfi da Jihar Katsina baki daya.
Shugaban na Karamar hukumar Kurfi ya mika godiyarsa ga DPO, Jami'an tsaron Farin kaya, SSS, Civil Defence Sarakunan gargajiya da sauran masu fada a ji na karamar hukumar ta kurfi.
A karshe Hon. Wurma ya nemi hadin kan jama'a da kira garesu da su dunga mika duk wani rahoto ko motsin da basu fahimta ba ga jami'an tsaro domin samun zaman lafiya mai ɗorewa a karamar hukumar Kurfi da jihar Katsina.