Magoya Baya Sun Haɗu Domin Jaddada Goyon Bayan Hon. Aliyu Abubakar Albaba a Katsina

Kakakin Majalisar Dokokin Katsina, Kwamishinoni da Jagororin APC Sun Bukaci A Sake Zaɓen Albaba a 2027Daruruwan magoya baya, shugabannin al’umma da jiga-jigan siyasa sun hallara a filin Makarantar Firamare ta…

Katsina City News June 21, 2026  ·  12:00 AM
| 37 Views
Magoya Baya Sun Haɗu Domin Jaddada Goyon Bayan Hon. Aliyu Abubakar Albaba a Katsina
Magoya Baya Sun Haɗu Domin Jaddada Goyon Bayan Hon. Aliyu Abubakar Albaba a Katsina


Kakakin Majalisar Dokokin Katsina, Kwamishinoni da Jagororin APC Sun Bukaci A Sake Zaɓen Albaba a 2027

Daruruwan magoya baya, shugabannin al’umma da jiga-jigan siyasa sun hallara a filin Makarantar Firamare ta Garama da ke kan titin Rafin Dadi a birnin Katsina ranar Lahadi, 21 ga Yuni, 2026, domin jaddada goyon bayansu ga ɗan Majalisar Dokokin Jihar Katsina mai wakiltar Mazabar Katsina (Cikin Birni), Hon. Aliyu Abubakar Albaba.


Taron, wanda al’ummar Unguwar Albaba, Rafin Dadi da Gwabron Gida suka shirya, ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na jihar, inda suka yabawa irin ayyukan da Hon. Albaba ya gudanar tare da kira ga al’umma su ci gaba da mara masa baya.


Babban baƙon taron shi ne Rt. Hon. Nasiru Yahaya Daura, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina kuma ɗan takarar Sanata na Shiyyar Daura.


Da yake jawabi, Mai Bai Wa Gwamnan Jihar Katsina Shawara Kan Wutar Lantarki da Makamashi, Dr. Hafiz Ibrahim Ahmad, ya jaddada muhimmancin zaɓen shugabanni nagari, yana mai cewa Hon. Aliyu Abubakar Albaba ya cancanci ci gaba da wakiltar al’ummar Katsina a Majalisar Dokokin Jiha.


Ya ce gwamnatin Malam Dikko Umar Radda ta himmatu wajen jawo masu zuba jari zuwa jihar tare da samar da ayyukan yi ga matasa ta hanyar shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arziki, ciki har da samar da kayayyakin aiki masu amfani da hasken rana da inganta wutar lantarki.


A nasa jawabin, Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Katsina, Alhaji Mannir Ayuba Sullubawa, wanda ya wakilci Gwamna Dikko Umar Radda, ya bayyana cewa yawan jama’ar da suka halarci taron alama ce ta irin kyakkyawar alaƙa da amincewar da al’umma ke da ita ga Hon. Albaba.


Ya ce wannan babban goyon baya da jama’a suka nuna ya tabbatar da cewa ɗan majalisar ya samu karɓuwa a tsakanin al’umma, tare da kira ga jama’a su ci gaba da mara masa baya.


Sullubawa ya kuma bayyana irin nasarorin da gwamnatin Malam Dikko Umar Radda ta samu a fannoni daban-daban na raya ƙasa, yana mai kira ga al’umma su ci gaba da goyon bayan jam’iyyar APC domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.


Shi ma Hon. Bashir Gafiya, wanda ya wakilci Ministan Gidaje da Raya Birane na Ƙasa, Engr. Muttaqa Rabe Darma, ya ce ayyukan Hon. Albaba sun wuce iyakokin Ƙaramar Hukumar Katsina, domin sun amfanar da al’umma a sassa daban-daban na jihar.


Ya buƙaci magoya baya su ci gaba da haɗa kai domin tabbatar da nasarar ɗan majalisar a zaɓe mai zuwa.

Advertisement


A nasa bangaren, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Katsina, Mustapha Kofar Bai, ya ce Hon. Albaba ba ya buƙatar talla saboda ayyukansa sun bayyana karara ga kowa.


Taron ya kuma samu jawaban goyon baya daga Sarkin Zango na Katsina, Alhaji Lawal Abu Yantaba, tsohon Kwamishina Alhaji Usman Nadada, wakilan tsohon Mataimakin Gwamna Alhaji Mannir Yakubu, Magajin Garin Katsina da sauran shugabannin al’umma.


Wakilin Haruna Maiwada Darakta Janar na gidan Dan'amana Movement honorabul Makiyu 

ya bayyana cewa ƙungiyar ta shirya tsaf domin tallafawa Gwamna Dikko Umar Radda, ɗan takarar Majalisar Tarayya Abba Mangal da Hon. Aliyu Abubakar Albaba a zaɓen 2026.


Ya kuma yi kira ga al’umma da su tabbatar sun mallaki katin zaɓe na dindindin (PVC), yana mai cewa hakan ne ginshikin samun nasara a babban zaɓe.


Da yake nasa jawabin, Rt. Hon. Nasiru Yahaya Daura ya yi kira ga jama’a su zaɓi jam’iyyar APC daga sama har ƙasa, tare da mara baya ga Hon. Aliyu Abubakar Albaba domin ci gaba da wakiltar Mazabar Katsina a Majalisar Dokokin Jiha.


Ya kuma buƙaci a zaɓi Abba Mangal a Majalisar Tarayya da Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua domin wakiltar Shiyyar Katsina a Majalisar Dattawa.


Kakakin Majalisar ya yabawa Hon. Albaba bisa irin ƙudurori da ayyukan alheri da ya gabatar a Majalisar Dokokin Jiha, yana mai addu’ar Allah Ya saka masa da alheri tare da cika masa burinsa.


A nasa jawabin na godiya, Hon. Aliyu Abubakar Albaba ya nuna farin cikinsa da irin gagarumin goyon bayan da al’ummar Katsina suka nuna masa.


Ya yi alƙawarin ci gaba da gudanar da ayyukan raya al’umma da wakilci nagari, yana mai tabbatar da cewa zai ci gaba da kare muradun al’ummarsa tare da kawo ayyukan ci gaba ga mazabarsa.


Taron ya ƙare da addu’o’i na neman zaman lafiya a Jihar Katsina, nasarar gwamnatin Malam Dikko Umar Radda da kuma samun nasarar jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2026.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 3 + 9?