Kungiyar Ma'aikatan KEDCO da SSAEAC Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai-baba-ta-gani.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes22012026_152119_FB_IMG_1769095239137.jpg



Daga Auwal Isah Musa

Kungiyar Manyan Ma’aikatan Wutar Lantarki da Kamfanonin Hadin Gwiwa (SSAEAC) tare da Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Kasa a Kano (KEDCO), sun shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani, lamarin da ya haddasa katsewar wutar lantarki a Kano, Katsina da Jigawa; jihohin da kamfanin na KEDCO ke kula da su.

Kungiyoyin ma’aikatan sun ce sun dauki matakin tsunduma yajin aikin ne bayan cikar wa’adin da suka bai wa shugabancin KEDCO, ba tare da cimma matsaya kan bukatunsu ba.

A cewarsu, sun shafe lokaci mai tsawo suna mika korafe-korafe kan rashin kyawun yanayin aiki da walwalar ma’aikata, gazawar hukumar kamfanin wajen biyan bukatun ma'aikata, rashin samun masoshi masu gamsarwa daga shugabancin kamfanin kan wasu bayanai da sauransu.

Da yake zantawa da manema labarai, mataimakin shugaban kungiyar SSAEAC na kasa a yankin Arewa, Rilwan Shehu, ya bayyana damuwarsa kan matsalar da haifar da rashin daidaito tsakanin ma’aikatan kamfanin da shugabanci, yana mai kira ga bangarorin biyu da su gaggauta nemo mafita domin kauce wa kara jefa al’umma cikin wahala.

Sai dai a martanin da ya mayar a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, shugabancin KEDCO ya bayyana cewa yawancin korafe-korafen da ma’aikatan ke gabatarwa tsofaffin batutuwa ne, yana mai jaddada cewa kamfanin na ci gaba da daukar matakai domin inganta jin dadin ma’aikata tare da magance matsalolin da ake fuskanta.

A Katsina, Jaridar Katsina Times ta kai ziyara ofishin KEDCO da ke Katsina domin jin karin bayani kan tsunduma shiga yajin aikin. Daya daga cikin ma’aikatan da muka taras, ya shaida mana cewar, “Mun samu umarnin shiga yajin aiki”, ya fadi yana kulle ofishin.

Muddin yakin aikin ya ci gaba ba tare da warware shi ba cikin lokacin, lamarin zai iya jefa jihohin uku cikin matsanancin duhu wanda hakan kan iya shafar yanayi kasuwanci musamman wadanda suka fi dogara da wutar ta lantarki.

Follow Us