AN KASHE ABDU LANKAI, SHUGABAN 'ƳAN BINDIGA DA YA AMSHI SULHU A JIBIYA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes28012026_080046_IMG-20260128-WA0017.jpg


Daga Mu’azu Hassan | Katsina Times/Katsina City News Facebook 

Rahotannin da Katsina Times ke samu sun tabbatar da mutuwar Abdu Lankai, wanda aka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagororin ƴan bindiga a yankin Jibiya, kuma wanda ya amshi sulhu da al’ummar ƙaramar hukumar.

Majiyoyi sun bayyana cewa rikicin ya samo asali ne tun daga ranar Juma’a zuwa ƙarshen makon da ya gabata, biyo bayan saɓani tsakanin ɓangaren Abdu Lankai da wasu ƙungiyoyin ƴan bindiga karkashin jagorancin Dogo Rabe da wani da ake kira Black, wanda ake zargin yana da alaƙa da Bello Turji.

A cewar majiyoyin, an zargi Abdu Lankai da hana wasu dabbobi da aka sato wucewa zuwa yankunan da ke Zamfara, abin da ya tayar da husuma tsakanin ɓangarorin. An ce wannan saɓanin ya ƙara tsananta ne duk da yunƙurin wasu fitattun shugabannin ƴan bindiga na tsawatarwa domin dakatar da rikicin.

Katsina Times ta ruwaito cewa an shirya zaman sulhu tsakanin shugabannin ƙungiyoyin uku, Abdu Lankai, Dogo Rabe da Black, a ranar Talata, 27 ga Janairu, 2026. Sai dai majiyoyi sun ce yayin zaman, ɓangaren Dogo Rabe ya zo da rinjaye, lamarin da ya rikide zuwa faɗa. Daga bisani aka kama Abdu Lankai, kuma a daren ranar aka tabbatar da mutuwarsa.

Abdu Lankai ya shahara ne a yankin Jibiya sakamakon rawar da ya taka wajen amincewa da sulhu, inda ya hana ayyukan ta’addanci a yankin da ke ƙarƙashinsa. Al’ummar Jibiya sun shaida wa Katsina Times cewa tun bayan cimma sulhun, yankin ya samu gagarumin sauƙin tsaro, abin da ya sa ake kallonsa a matsayin abin koyi.

Wasu mazauna yankin sun ce Abdu Lankai ya taka rawa wajen dakile wasu ƴan bindiga da ke ƙoƙarin rusa sulhun da aka cimma, lamarin da ya taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a ƙaramar hukumar.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Katsina Times ta yi ƙoƙarin jin ta bakin hukumomin ƙaramar hukumar Jibiya da jami’an tsaro, amma ba a samu nasara ba. Sai dai wasu mazauna ƙauyukan da ke yankin sun tabbatar da jin harbe-harben bindiga da kuma kiran ɗaukar fansa a daren mutuwarsa.

Masu sharhi na ganin cewa makomar sulhun da aka cimma a Jibiya yanzu ta rataya ne a kan yadda al’amura za su kasance bayan mutuwar wanda ya kasance jigon tsarin.

Katsina Times
www.katsinatimes.com
Facebook: Katsina City News
Jaridar Taskar Labarai

Follow Us