Dan Majalisar Dokoki Ya Dauki Nauyin Horas da Matasa 25 a Katsina, Ya Ba Su Tallafin Kayan Aiki

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes18012026_153635_FB_IMG_1768750455358.jpg

Daga Wakilinmu | Katsina Times

Dan Majalisar Dokoki mai wakiltar karamar hukumar Katsina, Honarabul Aliyu Abubakar Albaba, ya dauki nauyin horas da matasa 25 a fannoni daban-daban na sana’o’in dogaro da kai, tare da ba su tallafin kayan aiki domin su fara sana’a bayan kammala horon.

Horarwar, wadda ta shafe tsawon watanni uku ana gudanar da ita, ta kunshi koyar da gyaran firinji, na’urorin sanyaya daki (AC), injinan wanki (washing machines), da kuma yadda ake sanya iskar gas (refilling) a firinji da AC. An kammala horon ne a ranar Lahadi, 18 ga Janairu, 2026, a karkashin kulawar kamfanin SK Gidan Sanyi.

Da yake jawabi a wajen bikin kammala horon da yaye wadanda suka amfana, Hon. Aliyu Abubakar Albaba ya bayyana cewa shirin na daga cikin kudurorinsa na tallafa wa matasa domin rage zaman kashe wando da kuma karfafa tattalin arzikin al’umma ta hanyar dogaro da kai.

Ya tabbatar wa mahalarta taron cewa wannan shiri ba zai tsaya a nan ba, inda ya ce nan gaba akwai shirin horas da karin matasa 100 maza 50 da mata 50, domin su ma su amfana da irin wannan horo.

Sai dai dan majalisar ya gargadi wadanda suka amfana da shirin da su dauki sana’ar da muhimmanci, musamman wajen rike kayan aikin da aka ba su. Ya ce duk wanda aka samu ya sayar da kayan aikin da aka ba shi, hakan zai rage musu kwarin gwiwa na ci gaba da gudanar da irin wannan tallafi a nan gaba.

“Wannan shiri mun yi shi ne domin ku dogara da kanku. Idan muka samu labarin ana sayar da kayan da aka bayar, hakan zai sa mu yi shakku wajen ci gaba da irin wannan tallafi,” in ji Albaba.

Hon. Albaba ya kara da cewa yana da tsare-tsaren koyar da sauran sana’o’i kamar dinki da makamantansu domin kara bai wa matasa da mata damar dogaro da kai.

Matasan da suka ci gajiyar horon sun hada da maza 20 da mata biyar, inda aka tabbatar da cewa sun samu kwarewa a fannin gyaran firinji, AC, injinan wanki, da kuma sanya iskar gas cikin na’urorin sanyaya daki.

A nasa bangaren, shugaban kamfanin SK Gidan Sanyi, wanda aka gudanar da horon a karkashinsa, ya bayyana cewa kofofin kamfaninsu a bude suke ga matasan jihar Katsina domin kara musu kwarewa da gogewa a sana’o’in dogaro da kai. Ya kuma sanar da daukar mutum biyar daga cikin wadanda suka kammala horon aiki a kamfanin, a matsayin kara musu kwarin gwiwa.

Taron ya samu halartar manyan ’yan kasuwa da masu ruwa da tsaki daga karamar hukumar Katsina, ciki har da abokan Hon. Aliyu Abubakar Albaba, inda suka bayar da gudummawar kudi domin kara karfafa wa matasan gwiwa.

Daga cikin wadanda suka halarta da bayar da gudummawa akwai Alhaji Ahmad Gege, Alhaji Abu ’Yantaba, Alhaji Ali Kaura, Shugaban Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Katsina (KASSAROTA), Mejo Garba Yahaya Rimi (mai ritaya), Alhaji Aminu A.A. Rahamawa, Shugaban Jam'iyyar APC na karamar hukumar Katsina Alhaji Mustapha Kofar Bai, da sauran manyan baki.

An gudanar da taron ne a dakin taro na Government Day Secondary School, Kofar Yandaka, da ke kan titin Batsari a birnin Katsina. A yayin taron, kowanne daga cikin wadanda suka kammala horon ya samu na’urar zuba gas tare da tallafin kudi domin fara sana’a da dogaro da kai.

Follow Us