Gwamnatin Katsina Ta Kara Bude Kwalejin Kiwon Lafiya 5 Bisa Sharadi, 17 Zasu kasance a Rufe.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes24122025_185658_FB_IMG_1766602568435.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayar da umarnin ci gaba da rufe kwalejojin koyon kiwon lafiya masu zaman kansu 17 da suka kasa cika ƙa’idojin aiki, tare da ba da izinin buɗe wasu biyar bisa sharaɗi, a ranar Laraba.

Da yake jawabi ga manema labarai a Sakatariyar Jiha, Mai Bai wa Gwamna Shawara na Musamman kan Kiwon Lafiya da Manyan Makarantu, Hon. Umar Mammada, ya ce matakin ya biyo bayan amincewar Majalisar Zartarwar Jihar da rahoton Kwamitin Aiki na Ma’aikatu da dama, a zamanta na 10 ga Disamba, 2025.

Mammada ya bayyana cewa kwalejojin biyar da aka ba izinin buɗewa bisa sharaɗi sun cika mafi ƙarancin buƙatun aiki, amma dole ne su samu cikakkiyar sahalewar NBTE kafin ƙarshen kwata na farko na shekarar 2026. Ya jaddada cewa an takaita izinin ne ga wasu darussa kaɗan, inda ya gargaɗi cewa rashin bin sharaɗan zai kai ga janye amincewar.

Ya ƙara da cewa kwalejoji 17 da suka kasa gyara kura-kuran da kwamitin ya gano za su ci gaba da kasancewa a rufe, yayin da makarantu biyu da aka gano suna aiki ba bisa ƙa’ida ba aka umarce su da su rufe nan take.

A cewarsa, daga yanzu makarantun da suka samu sahalewa kaɗai, tare da amincewar Ma’aikatar Lafiya, ne za su iya tura ɗalibansu zuwa aikin horaswa (practical), a wani yunƙuri na ƙarfafa kulawa da inganta ƙa’idojin koyar da kiwon lafiya.

“Gwamnatin Jihar Katsina ba za ta yi sassauci ba kan inganci da tsaro a fannin horas da ma’aikatan kiwon lafiya,” in ji Mammada.

Matakin na daga cikin ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Katsina na tsaftace harkar makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu da kuma inganta ingancin ma’aikatan kiwon lafiya a fadin jihar.

Makarantun da suka samu izinin budewa bisa Sharadi sun hada da GIAL College of Health, Cognate Collage of Health Sciences, Kebram College of Health, Barda Collage of Health Sciences, da Alliance College of public and environmental health.

Follow Us