Rahoton SBM Intelligence: Yadda ’Yan Bindiga Suka Karɓi Sama da Naira Biliyan 2.5 na Fansa Cikin Shekara Ɗaya a Najeriya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes24122025_124157_b_Create_a_professiona (2).png

Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times

Wani rahoto mai zurfi da cibiyar bincike mai zaman kanta, SBM Intelligence, ta fitar ya nuna yadda matsalar garkuwa da mutane ta ƙara tsananta a Najeriya, inda ’yan bindiga suka karɓi aƙalla Naira biliyan 2.57 a matsayin kudin fansa tsakanin Yuli 2024 zuwa Yuni 2025.

Rahoton, wanda aka fitar a ranar 19 ga Disamba, 2025, ya yi nazari kan manyan al’amuran siyasa, tsaro da tattalin arziki da suka shafi Afirka a shekarar 2025, tare da mayar da hankali sosai kan yadda sace-sace ke zama wata babbar masana’antar aikata laifi a Najeriya.

A cewar rahoton, duk da cewa masu garkuwa da mutane sun nemi kusan Naira biliyan 48 a matsayin kudin fansa daga iyalai da al’ummomin da abin ya shafa, abin da aka samu a zahiri bai wuce ƙaramin kaso daga cikin wannan adadi ba. Wannan na nuni da cewa, ko da yake ana ta neman makudan kudade, yawancin waɗanda abin ya shafa ba su iya biyan abin da ake nema ba.

Masana sun bayyana cewa wannan gibi tsakanin abin da ake nema da abin da ake samu na iya haifar da ƙarin tashin hankali, saboda ’yan bindiga kan ƙara tsaurara matakai ko tsawaita lokacin tsare waɗanda suka sace.

Rahoton SBM Intelligence ya jaddada cewa garkuwa da mutane na da mummunan tasiri ga rayuwar al’umma, musamman a jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, inda ake yawan samun irin waɗannan laifuka. An bayyana cewa iyalai da dama kan sayar da kadarorinsu, kayan noma da dabbobi domin tara kudin fansa, lamarin da ke ƙara jefa su cikin talauci.

Haka kuma, rahoton ya nuna cewa tsoron sace mutane ya rage zirga-zirgar kasuwanci, ya hana zuba jari, tare da raunana amincewar jama’a da ikon gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyi.

SBM Intelligence ta yi kira ga gwamnati a matakai daban-daban da ta ƙara inganta dabarun tsaro, haɗa bayanan sirri, da kuma magance tushen matsalar ta hanyar samar da ayyukan yi, rage talauci da kuma ƙarfafa hukunci ga masu aikata laifuka.

Masu sharhi kan harkokin tsaro sun shaida wa Katsina Times cewa muddin ba a ɗauki matakan gaggawa ba, garkuwa da mutane na iya ci gaba da zama wata hanya ta samun kuɗi ga ƙungiyoyin masu laifi, lamarin da zai ƙara dagula zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Follow Us