Majigiri Ya Shigar da Kudirin Kafa Kwalejin Jinya a Mashi, Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes23122025_183149_Screenshot_20251223-193111.jpg



Katsina Times

Hon. Salisu Yusuf Majigiri, wanda ke wakiltar kananan hukumomin Mashi da Dutsi a Majalisar Wakilai, ya shigar da Kudirin Kafa Kwalejin Kiwon Lafiya da Jinya ta Gwamnatin Tarayya, Mashi, Jihar Katsina (HB.1554), ta hanyar karatu na farko, na biyu da na uku a Majalisar.

Kudirin na da nufin kafa wata kwaleji ta musamman da za ta dinga horar da ma’aikatan jinya, domin magance karancin kwararru a fannin kiwon lafiya a Jihar Katsina da kuma Najeriya baki ɗaya.

Ci gaban dokar ya samu ne bayan cikakken nazari da Kwamitin Majalisar kan Harkokin Cibiyoyin Lafiya, karkashin jagorancin Hon. Patrick Umoh. Kwamitin ya gudanar da nazari kan dokoki makamantan haka, ciki har da kafa Cibiyoyin Lafiya na Tarayya a Borno da Bauchi, da kuma Kwalejojin Kiwon Lafiya da Jinya a Jihar Akwa Ibom.

Masana fannin kiwon lafiya na ganin cewa kafa kwalejin a karamar hukumar Mashi zai bai wa matasa na gida damar samun horo mai inganci, rage wahalar tafiya nesa domin karatu, da kuma inganta lafiyar uwa da yara a yankin.

A halin yanzu, dokar na jiran amincewa a hukumance kafin ta zama doka, wanda hakan zai zama muhimmin mataki wajen karfafa ma’aikatan kiwon lafiya a Najeriya da fadada damar ilimi a yankuna daban-daban.

Majigiri ya ce “Samar da wannan makaranta mataki ne mai muhimmanci wajen horar da matasa da basu kwarewa domin inganta kiwon lafiya da kuma tabbatar da jin dadin al’umma.”

Follow Us