"Zakka da Waqafi Muhimman Hanyoyi ne na Yaki da Talauci” — Gwamna Radda A Taron Ƙasa na AZAWON karo na 5

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes22122025_185454_FB_IMG_1766429614651.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times 

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya bayyana Zakka da Waqf a matsayin muhimman ginshiƙai wajen yaki da talauci, rashin daidaito da zalunci a al’umma, inda ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ƙarfafa tsarin Zakka mai nagarta a jihar.

Gwamna Radda ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 22 ga Disamba, 2025, yayin da yake jawabi a wajen Taron Ƙasa na Biyar na Ƙungiyar Masu Gudanar da Zakka da Waqf a Nijeriya (AZAWON), wanda aka gudanar a Hillside Conference Hall, Katsina.

Gwamnan ya ce karɓar bakuncin taron ƙasa a Katsina wata babbar alama ce a tarihin jihar, yana mai cewa an kawo taron jihar ne domin ƙarfafa tsarin Zakka da Waqf.

“Yau rana ce mai matuƙar muhimmanci a tarihin jiharmu. Karɓar bakuncin wannan taro ba abu ne da za mu ɗauka da wasa ba, domin sakamakonsa zai daɗe yana anfani ga jihar,” in ji Radda.

Ya bayyana cewa kafa Hukumar Zakka da Waqf ta Jihar Katsina ba ta zo ne bisa wata manufa ba, illa tsari ne da aka tsara domin rage talauci, kawar da rashin adalci, da tallafa wa marasa ƙarfi.

“Kafuwar hukumar Zakka da Waqf a Katsina an yi ta ne domin fuskantar matsalolin talauci da kuma taimaka wa waɗanda ke cikin tsananin buƙata,” in ji gwamnan.

Gwamna Radda ya ce cikin kusan shekaru biyu da fara aiki, hukumar ta samu nasarori masu yawa ƙarƙashin jagorancin shugabanta, inda ya yaba wa shugaban hukumar, mambobin kwamitin gudanarwa da ma’aikata bisa jajircewarsu da gaskiya.

Ya kuma yi bayani kan shirye-shiryen gwamnatinsa na rage talauci, inda ya ce jihar ta ware sama da naira biliyan 10 domin tallafa wa ƙananan sana’o’i da matsakaita (MSMEs), lamarin da ya sanya Katsina cikin jihohin da suka fi kashe kuɗi a wannan fanni a ƙasar.

Haka kuma, gwamnan ya bayyana cewa shirin tallafa wa mata da gwamnatinsa ta ƙaddamar a farkon shekarar nan, wanda ya lakume kusan naira biliyan 5.7, ya amfani mata fiye da 40,000 a fadin jihar.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta raba kayan abinci ga sama da gidaje 90,000 na marasa galihu, tare da zuba sama da naira biliyan 70 wajen inganta noma da samar da kayan aikin noma ga manoma ƙanana, matsakaici da manya.

A cewarsa, wadannan matakai ne suka taimaka wajen samun amfanin gona mai yawa a jihar a bana, la’akari da cewa sama da kashi 90 cikin 100 na al’ummar Katsina na dogaro da noma.

A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar AZAWON na Ƙasa kuma Shugaban Hukumar Zakka da Waqf ta Jihar Sakkwato, Muhammad Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato, ya ce tarurrukan ƙungiyar na baya sun kafa tubali mai ƙarfi wajen inganta tsarin Zakka da Waqf a Nijeriya.

Ya bayyana cewa duk da albarkar ɗan Adam da na ƙasa da Allah Ya yi wa Nijeriya, ƙasar na fama da manyan ƙalubalen tattalin arziki, ciki har da talauci da rashin aikin yi.

“Fiye da ‘yan Nijeriya miliyan 133 na fama da talauci iri-iri, yayin da rashin aikin yi tsakanin matasa ya haura kashi 30 cikin 100. Wadannan ba alkaluma kawai ba ne, mutane ne na gaske da iyalai masu fama da ƙuncin rayuwa,” in ji shi.

Maidoki ya jaddada cewa tsarin tattalin arzikin Musulunci — musamman Zakka, Waqf da Sadaka — na da cikakkiyar mafita wajen rage talauci da rashin daidaito.

A cewarsa, tun bayan kafa AZAWON da tsara tsarin Zakka da Waqf a fadin ƙasar, mambobin ƙungiyar sun tara sama da naira biliyan 10 na Zakka, naira biliyan 3.7 na Waqf, da kuma kusan naira miliyan 465 na Sadaka, inda aka raba wa mabukata a fadin Nijeriya.

Ya bayyana hakan a matsayin nasara da ba a taba samun irinta ba a Nijeriya da ma yankin Yammacin Afirka.

Shi ma Shugaban Hukumar Zakka da Waqf ta Jihar Katsina, Dakta Ahamed Filin Samji, ya yaba wa Gwamna Radda bisa kafa tsari mai inganci da gaskiya na Zakka a jihar. Ya ce hukumar ta inganta gaskiya da daidaito wajen karɓa da rabon Zakka, tare da tabbatar da cewa kuɗaɗen sun isa ga waɗanda suka cancanta bisa koyarwar Musulunci.

Hakazalika, Sarkin Kazaure, Alhaji Adamu Abubakar, wanda ya wakilci Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga Musulmi da su cika farali na Zakka tare da rungumar Waqf a matsayin sadaka mai gudana da alherinta ke dorewa bayan rayuwa.

Taron ya samu halartar wakilan gwamnonin jihohin Kano, Neja, Kaduna da Jigawa, sarakunan gargajiya ciki har da hakimai da dagatai, wakilan Sarkin Katsina da Sarkin Daura, da kuma Musulmi daga sassa daban-daban na Nijeriya da ma Jamhuriyar Nijar.

Follow Us