Kasafin Kuɗin 2026 Tarkon Bashi Ne, Ba Gyara Ba – ADC

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes22122025_173249_FB_IMG_1766424727340.jpg



Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta soki kudirin kasafin kuɗin shekarar 2026 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar, tana mai cewa kasafin tarkon bashi ne da aka lullube da sunan gyara, wanda ya dogara da karɓar rance fiye da kima da kuma hasashen kudaden shiga da ba su da tabbas.

A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Ƙasa na jam’iyyar, Malam Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Litinin, ADC ta ce kasafin kuɗin na Naira tiriliyan 58.18 bai zo da wani sabon salo ba, illa ci gaba da abin da ta bayyana a matsayin sakaci wajen tafiyar da kuɗaɗen gwamnati.

Jam’iyyar ta ce irin wannan kasafi ya yi kama da na shekarun 2024 da 2025, waɗanda, a cewarta, yawancin ayyukan da aka tsara a cikinsu ba a aiwatar da su yadda ya kamata ba.

ADC ta kuma ce duk da ikirarin gwamnati na ware Naira tiriliyan 25.68 domin ayyukan raya ƙasa, gibin kasafin da ya kai Naira tiriliyan 23.85 na nuna cewa kusan dukkan ayyukan za a aiwatar da su ne ta hanyar karɓar bashi mai tsada.

Jam’iyyar ta yi gargadin cewa wannan tsari na iya ƙara jefa Nijeriya cikin matsanancin hali na tattalin arziki, tare da ɗaure makomar al’ummomi masu zuwa, idan har ba a sake duba tsarin kasafin da manufofin kuɗi ba.

Follow Us