Yadda Aka Yamutsa Tsakanin Obasanjo da Atiku

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes21122025_182906_IMG-20251221-WA0192.jpg

Daga Mu’azu Hassan @Katsina Times

A cikin littafin ACCORDING TO THE PRESIDENT, wanda tsohon mai magana da yawun Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya wallafa, marubucin ya bayyana tarihin rayuwarsa, shigarsa aikin jarida, da darussan da ya koya a tsawon hidimarsa.

Littafin, mai shafuka 255, wanda aka ƙaddamar da shi a tsakiyar shekarar 2025, ya yi bayani dalla-dalla kan wasu muhimman abubuwa da suka faru a lokacin da Garba Shehu ke aiki tare da Atiku Abubakar, a zamaninsa na mataimakin shugaban ƙasa ƙarƙashin Olusegun Obasanjo.

A cewar Garba Shehu, dangantaka ta yi tsami matuƙa tsakanin Obasanjo da Atiku, wato shugaban ƙasa da mataimakinsa. Lamarin ya kai Atiku ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Daga nan PDP ta bayyana cewa ficewarsa daga jam’iyya ya sa ya rasa kujerarsa ta mataimakin shugaban ƙasa. 

Rahoton ya ce an rage yawan jami’an tsaron da ke tare da shi, tare da yunƙurin sauya shi a ofis.

A wannan lokaci Atiku na ƙasashen waje, inda aka sanar da shi ya dawo Nijeriya ta jirgin kasuwanci. Da dawowarsa, ya shigar da ƙara a Supreme Court of Nigeria.


Littafin ya bayyana cewa kafin Kotun Ƙoli ta yanke hukunci, an turo wasu sojoji da zargin an yi hakan ne da niyyar hallaka Atiku. Wannan ya sa ya shiga ɓoye, inda ya tafi jihar Benue cikin sirri, ya ɓuya a gidan Gwamnan jihar a wancan lokaci, George Akume.

Bayan kwanaki Fadar Shugaban Ƙasa ta rasa inda mataimakin shugaban ƙasa yake, abin da ya jefa su cikin fargaba. 

Mutanen Atiku suka fitar da sanarwar manema labarai cewa rayuwarsa na cikin haɗari. Wannan ya sa gwamnati ta fitar da sanarwa cewa za ta ba shi dukkan kariyar tsaro da ta dace. Daga nan ne Atiku ya fito daga maɓoyarsa.

A makon da Kotun Ƙoli za ta yanke hukunci kan matsayinsa, ƙasar ta ɗau zafi. Atiku ya fitar da dukkan kayansa daga gidan gwamnati da ofishinsa. 

Garba Shehu ya ce wata rana da farkon dare Atiku ya kira shi; shi da matarsa Jamila suka shiga motarsa, yayin da jami’an tsaro da sauran tawaga ke bin su a baya.

Sun yi yawo a cikin Abuja, daga bisani Atiku ya umarci a tsayar da mota, inda dogarinsa daga Department of State Services (DSS) ya zo, aka umarce su da su daina bin su. 

Daga nan Atiku ya tabbatar babu mai bin su, suka wuce ta wata hanya har suka isa rukunin gidajen ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja, inda suka sauka a wani gida kafin Garba Shehu ya bar su.

Bayan Kotun Ƙoli ta yanke hukunci cewa shugaban ƙasa ba shi da ikon tsige mataimakinsa sai an bi tanadin kundin tsarin mulki, Garba Shehu ya ce ya je ya ɗauko Atiku da matarsa daga inda suka ɓuya zuwa gidansa da ke fadar shugaban ƙasa.

Atiku ya kammala wa’adinsa tare da Obasanjo, amma a jam’iyyu daban-daban: Obasanjo a PDP, Atiku kuma a Action Congress of Nigeria (ACN)

Katsina Times 
@ www.katsinatimes.com 
Facebook; katsina city news 
Social media handles...katsina Times 
07043777779

Follow Us