Me Ya Sa Aka Yi Ƙoƙarin Dukan Hadi Sirika a Dutsi?

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes17122025_190251_Hadi-Sirika-Minister-of-Aviation.jpg


@Katsina Times

A ranar Talata, 16 ga watan Disamba, tsohon Sanata, kuma tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Alhaji Hadi Sirika, ya sha da ƙyar a hannun wasu mutanen garin Dutsi da ke Jihar Katsina, lokacin da ya je halartar jana’izar Marigayi Marusan Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya fara ne bayan Hadi Sirika ya isa fadar masarautar yankin, inda ya samu wuri ya zauna. 

A cewar wani da abin ya faru a gabansa, wani mutum a cikin fadar ya kalli Hadi Sirika ya ce masa: “Me ya kawo ka nan? An gayyace ka ne?” Wani kuma ya buƙace shi da ya bar wajen.

Ana cikin haka ne labarin shigowar Hadi Sirika ya bazu, inda jama’a suka yi cincirindo a ƙofar fadar suna kiran a fito da shi domin a lakaɗa masa duka. 

Wasu daga cikin fusatatun sun riƙa furta kalamai marasa daɗi, kamar yadda aka ji kuma aka gani a wani bidiyo da aka ɗauka da waya a daidai lokacin.

Jama’a sun tare ƙofar shiga fadar, suka hana masu fusatattun shiga su cimma Hadi Sirika. 

Duk ƙoƙarin da aka yi na rarrashi da watse jama’ar ya ci tura, domin sun dage sai an fito da shi a koya masa hankali!

Hayaniya da yamutsi suka ci gaba har zuwa isowar Mai Martaba Sarkin Katsina. 

Duk da zuwan jami’an tsaro, jama’a sun ƙi barin harabar fadar.

Ganau sun shaida cewa ba a samu fitar da Hadi Sirika daga fadar ba sai bayan da aka fara jana’izar mamacin. Yayin da jama’a suka mai da hankalinsu wajen Sallah, aka fitar da shi aka saka shi cikin wata mota ya bar fadar.

Wasu daga cikin jama’ar sun yanke Sallar jana’izar suka bi motar da ihu da kalamai marasa daɗi. Wannan ne ya haddasa rikici a wani lungu, inda aka sake samun hayaniya.

Me Ya Haddasa Wannan Fushi?

Wasu daga cikin mazauna Dutsi, da jaridar KATSINA TIMES ta tattauna da su, sun zargi cewa akwai tsohuwar gaba mai tsanani tsakanin Marigayi Marusan Katsina da Hadi Sirika. Sun ce marigayin ya sha wahala a zamanin tsohon Ministan kafin rasuwarsa.

Haka kuma, jama’ar Dutsi suna zargin Hadi Sirika da kasancewa kanwa uwar gami na rabuwar masarautarsu, inda aka yanke kashi mai tsoka aka ba wani a matsayin Hakimi. 

Sun ce wannan raba masarauta da suka ce Hadi Sirika ne ya haifar da ita, wanda ya jawo suke zaman doya da manja da rarrabuwar kawunansu da suka kwashe fiye da shekaru 100 suna zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

Sun ƙara da cewa bayan yanke ƙasar Marigayin, an riƙa bin sa da matsin lamba da ƙulle-ƙulle, har aka ce kada ya ƙara shiga fadar sarautar Katsina. Sannan aka buƙace shi ya bar gidansa da ke Dutsi da hujjar za a yi gyara.

Wasu daga cikin ‘yan uwan marigayin sun ce ya yi rashin lafiya na dogon lokaci, amma Hadi Sirika bai kai ziyara ko aika da Wakili ba. Sun ce sai a lokacin da marigayin ke kwance a asibiti, rai-kwakwai-mutu-kwakwai, ne Hadi Sirika ya je asibitin. Kwana guda bayan ziyarar tasa, Marusan Katsina ya rasu.

Martanin Hadi Sirika

Jaridar KATSINA TIMES ta tabbatar da cewa lamarin ya samo asali ne daga fushin sarauta, tare da zargin amfani da ƙarfi, matsin lamba da bita-da-ƙulli.

Jaridar ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Sanata Hadi Sirika, amma haƙarta ba ta cimma ruwa ba. An aike masa da saƙonni ta lambobin wayarsa, amma jba a samu amsa ba. 

Haka kuma, duk ‘yan uwa da makusantansa da aka tuntuɓa sun ce ba za su yi magana a kan lamarin ba, domin bai ba su izini ba.

Katsina Times 
@ www.katsinatimes.com.
Facebook: katsina city news 
All social media handles: katsina Times.
07043777779.

Follow Us