Majalisar Dattawa Za Ta Gudanar da Taron Musamman Don Karrama Marigayi Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes22072025_190923_FB_IMG_1753210965347.jpg


Majalisar Dattawan Najeriya ta sanar da shirinta na gudanar da zaman musamman a ranar Laraba, 23 ga Yuli, 2025, domin karrama marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu makon da ya gabata.

A zaman majalisar na ranar Talata, sanatoci sun yi jinjina ga marigayin tare da yabawa da irin gudunmawar da ya bayar ga ƙasa, sannan suka yi addu’ar samun rahama da sauƙin hisabi gare shi.

Haka zalika, majalisar ta karrama marigayi Oba Sikiru Adetona, Awujale na Ijebuland, da kuma fitaccen ɗan kasuwa mai taimakon al’umma daga Kano, Alhaji Alhassan Dantata. An gudanar yi shiru na dan lokaci domin girmama waɗanda suka rasu.

Ana sa ran zaman na musamman zai haɗa manyan jami’an gwamnati da baki na musamman domin bayyana girmamawa ga marigayi Buhari, wanda ya shugabanci Najeriya a matsayin shugaban soja da kuma shugaban ƙasa da aka zaɓa ta dimokuraɗiyya.

Follow Us