APC Ta Tsayar da Ranar 24 ga Yuli don Taron NEC na Zaɓen Sabon Shugaban Jam’iyya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes30062025_195906_APC.jpg

Katsina TIMES 

Jam’iyyar APC mai mulki ta sanar da cewa za ta gudanar da taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) a ranar 24 ga watan Yuli domin zaɓen sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Mataimakin Sakatare na ƙasa na jam’iyyar, Barista Festus Fuanter, ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan wani gaggawan taron Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Ƙasa (NWC) da aka gudanar a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja.

A cewarsa, “An riga an aika da takardar sanarwa zuwa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) dangane da taron NEC da za a gudanar, wanda zai bai wa jam’iyya damar zaɓen sabon shugaba.”

Ya ƙara da cewa: “Kamar yadda kuka sani, kwamitin NEC shi ne mafi girma a tsarin mulkin jam’iyyar. Don haka, duk wani mataki da za a ɗauka, musamman na tabbatar da sabon shugaban jam’iyyar, dole ne ya samu amincewar wannan kwamiti.”

Barista Fuanter ya ce idan a yayin taron NEC ‘ya’yan jam’iyyar sun amince da sabon ɗan takara, to jam’iyyar za ta karɓa, sannan a jira matakin ƙarshe da za a ɗauka dangane da sabon shugaban jam’iyya na dindindin.

Haka kuma, ya bayyana cewa taron NWC ya tattauna kan shirin zaɓen cike gurbi a wasu jihohi, inda ‘yan majalisar dokokin jiha da na tarayya suka rasu ko kuma suka yi murabus.

A ranar Juma’a, 27 ga Yuni, 2025 ne tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ajiye mukaminsa domin mayar da hankali kan wasu muhimman al’amuran kansa.

Follow Us