Zamu Yi Duk Mai Yiyuwa Wurin Farfado Da Martabar Sarakunan Gargajiya - Cewar Sanata Zangon Daura

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes27072025_171232_640px-NSZD_Portrait.png



Dan Majalissar Dattawa na Shiyyar Daura Sanata Nasiru Sani Zangon Daura,ya lashi takobin cewa zai bada duk goyon bayan da ya dace na farfado da martanar Sarakunan Gargajiya a Najeriya.

Sanata Zangon Daura ya tabbatar da hakan ne a sa'ilinda yake zantawa da Manema Labarai a lokacin taron jin ra'ayoyin al'umma na Shiyyar Arewa Maso Yamma akan gyaran Kundin Tsarin Mulkin Najeriya a Kano.

Sanata Nasiru Sani Zangon Daura ya nuna damuwa akan yadda kimar Sarakunan Gargajiya ta rage a Najeriya, wanda hakan ya sanya basu samun kular da ta dace.

"Rashin kasancewar su a tsarin tafiyar da al'amurran Kasa, na daga cikin abinda ya kara rura wutar matsalar tsaro a Najeriya, sabanin lokutan baya da suke da kima ta kowace fuska"cewar shi.

Dan Majalissar Dattawan ya ce a matsayin shi na mai ruwa da tsaki, zai ja hankalin abokan aikin shi Sanatoci akan su goyi bayan kudirin yin gyara ga dokar farfado da maratabat sarakunan, domin a samu mafita a halin da ake ciki.

Sanata Zangon Daura ya kuma magantu akan sha'anin da ya jibanci kirkiro da Jihar Bayajidda daga Jihar Katsina, gami da batun bada kashi 35 na Shugabanci ga mata a Najeriya.

Daga karshe ya yabawa Gwamna Dikko Radda akan kafa kwamitin nagartattu kuma kwararrun mutane, domin su kasance wakilan Jihar Katsina akan gyaran Kundin Tsarin Mulkin.

Follow Us