'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Masu yawa da sukai garkuwa da su a Zamfara

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes28072025_124023_img-20250211-wa0051_720.jpg


KatsinaTimes 

Wasu 'yan bindiga dauke da makamai, karkashin jagorancin wani shahararren ɗan ta'adda da ake kira Kachalla Bello, wanda kuma aka fi sani da Dansadiya, sun kashe mutane da dama da suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara, kamar yadda wasu da suka tsira suka bayyana.

Lamarin ya faru ne a kauyukan Yamutsawa da Banga da ke cikin karamar hukumar Kauran Namoda, inda aka ce 'yan bindigar sun yi garkuwa da sama da mutane 80 a hare-hare daban-daban da suka kai wa al'ummar kauyukan nan kwanan nan.

Wadanda suka tsira sun bayyana cewa yawan mutanen da aka kashe na iya kaiwa sama da 50. Wani mazaunin Banga ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa mutane 50 ne aka sace daga kauyen Banga, amma 18 kacal suka dawo da rai.

A cikin wadanda suka mutu har da jarirai uku da aka dade da yin garkuwa da su tare da iyayensu.

Haka zalika, daga cikin mutane 33 da aka sace a Yamutsawa, an bayyana cewa 20 sun mutu yayin da suke tsare a hannun 'yan bindigar.

Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan mutanen da aka kashe matasa ne masu shekaru tsakanin 17 zuwa 20, ciki har da mata hudu da kuma kananan yara.

Wani da ya tsira daga harin ya ce, “Wannan abin tsoro ne. An raba mu sassa daban-daban kuma aka rike mu tsawon lokaci a cikin mawuyacin hali.”

Wadanda suka tsira sun bayyana cewa Dansadiya yana tilasta wa fursunoni kashe wasu a gaban jama'a domin tsoratar da su. “Mafi munin abin da muka gani shi ne yadda Dansadiya ke umartar wasu daga cikin mu su kashe wasu da akai garkuwa da su,” in ji wani da ya tsira.

Dansadiya ya shahara wajen neman kudaden fansa masu yawa, kuma yana ci gaba da kashe wadanda ke hannunsa koda bayan an biya fansa.

Wani mazaunin yankin ya ce: “Akwai lokuta da dama da ya karɓi kuɗin fansa daga iyalan mutane, amma duk da haka sai ya kashe su.”

Ana danganta karuwar rashin tsaro a yankin da rashin kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin al’umma da jami’an tsaro, wanda ke kara tabarbarewar lamarin.

Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa, “Koda wani ya kira jami’an tsaro domin neman taimako, ba sa samun amsa cikin gaggawa saboda matsalar sadarwa da rashin fahimtar yaren juna.”

Kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ya ci tura, domin kakakin rundunar, SP Yazid Abubakar, bai amsa kiran waya da sakonnin da aka tura masa ba har zuwa daren jiya.

Follow Us