Muazu Hassan
@ Katsina Times
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Dakta Bashir Gambo Saulawa, ya bayyana wa jaridun Katsina Times cewa sun kai ƙarar wasu ’yan takarar da suka samu tikitin wasu jam’iyyu ne ba don komai ba sai don a bi doka kuma a kiyaye ta.
Bashir Gambo ya ce dokar zaɓe ta bayyana duk yadda za a shiga takara da kuma yadda za a gudanar da zaɓen shekarar 2027.
Dokar ta tsara jadawalin komai, da yadda za a gudanar da shi, da kuma lokacin da za a gabatar da shi. Mun gano cewa waɗannan ’yan takarar sun saɓa wa waɗannan ƙa’idojin zaɓe.
Gambo ya ce: “Dokar nan fa, tana a yanar gizo, kyauta za ka iya sauke ta. Kuma ana samun wadda aka buga.”
Gambo ya ce sun bi dokar nan, sun tabbatar a rubuce cewa an saɓa wa ƙa’ida. Saboda haka ne suka tafi kotu domin kotu ta yi musu adalci.
@ Katsina Times
Www.katsinatimes.com
Facebook Page: Katsina City News
Facebook Group: Katsina City News
Facebook Page: Jaridar Taskar Labarai


Comments (0)
No comments yet. Be the first to share your thoughts!