Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Hajiya Rakiya Hassan, wadda akafi sani da "R.K. Mai Waina – Hakuri Maganin Zaman Duniya", dattijuwa 'yar shekara 81, ta shahara a sana'ar sayar da waina a birnin Katsina, inda ta shafe fiye da shekaru hamsin tana hidima ga al'umma.
R.K. 'yar asalin karamar hukumar Kaita ce. Ga duk wanda ya san birnin Katsina tun shekaru hamsin da suka gabata, sunanta na daga cikin sunayen da suka kafa tarihi a fagen kasuwancin abinci, musamman waina da miya. Daga manyan mutane, sarakuna, 'yan siyasa, da masu mulki har zuwa talakawa – abincinta ne ya kasance zabin karin kumallo.
A wata tattaunawa da Katsina Times, Hajiya Rakiya ta bayyana cewa yanzu ta daina sana'ar saboda tsufanta da kuma matsalar ido. A halin yanzu tana zaune a unguwar Filin Fayis cikin birnin Katsina.
Ta bayyana cewa ba waina ta fara yi ba a matsayin sana’a. “Na fara ne da sayar da alkubus, daga baya sai na koma kan waina. Tabbas, na samu nasarar rayuwa a cikin wannan sana’a,” in ji ta. “A duk fadin jihar Katsina da jihohin makwabta, mutane suna sayen abincina. Na je Makka sau shida, kuma a cikin wannan sana’a ce duk wannan ya faru. Ko da Allah bai bani haihuwa ba, amma na reni ’ya’yan wasu, na aurar da su, har na kai su Makka. Alhamdulillah.”
Hajiya R.K. ta ce ta yi zamani da Sarkin Katsina, Marigayi Usman Nagogo, wanda ya kasance daya daga cikin kwastomominta, da kuma tsohon Gwamnan Kaduna, Marigayi Alhaji Lawal Kaita. “Na fara sana’ar ne da tiya daya ta alkama, da kwabo arba’in na rance – daga nan ne Allah ya ba ni sa’a har na kai ga nasara,” in ji ta.
Cikakken bayani da hira na musamman tare da Hajiya R.K. na samuwa a shafin Katsina Times YouTube da sauran kafafen sada zumunta.