Bayan cece-kuce da zanga-zanga; An tono gawar mawaki Mohbad da ake zargin akwai badakala cikin mutuwarsa
- Katsina City News
- 21 Sep, 2023
- 1109
Matashin mawakin mai shekaru 27 dake tashe musamman a kudancin Najeriya, magoya bayansa na ta gudanar da zanga-zanga sakamakon zargin cewa abokanan sana'arsa ta waka ne suka sa masa wani abu ya sha ya mutu, kamar yadda aka jiyo shi yana fada lokacin da yake kwance bisa asibiti
"Ƴan sanda a jihar Legas da ke Najeriya sun kammala tono gawar wani fitaccen mawaƙi a ƙasar, Ilerioluwa Aloba da aka fi sani da Mohbad, wanda ya mutu a makon da ya gabata, domin gudanar da binciken musabbabin mutuwarsa.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana haka cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
"An kammala tono gawar, yanzu za a fara gwaji don gano musabbabin mutuwarsa", kamar yadda ya wallafa.
Mawaƙin mai shekara 27, ya mutu ne ranar Talata 12 ga watan Satumba a wani asibiti a Legas, sai dai ba a bayyana abin da ya yi sanadin mutuwarsa ba.
Tun bayan mutuwar tasa, magoya bayansa a biranen kudancin Najeriya suka riƙa yin kiraye-kirayen yi masa adalci, musamman a shafukan sada zumunta.
Hukumomi a jihar Legas sun alƙawarta gudanar da bincike domin gano abin da ya yi sanadin mutuwarsa, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito"