Gidauniyar Garkuwa Ta Raba Tallafin Sallah Ga Mutane Fiye da 500 a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes01062025_163204_FB_IMG_1748795405957.jpg


Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times

Ahamed Dayyabu Safana 

Gidauniyar Garkuwa karkashin jagorancin tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Batsari, Safana da Danmusa a jihar Katsina, Hon. Ahmed Dayyabu Safana, ta raba tallafin Sallah ga fiye da mutum 500 a wani bangare na shirin jin ƙai da taimakon al’umma domin saukaka musu bukukuwan Sallah da ke tafe.

An gudanar da rabon tallafin ne a ranar Lahadi, 1 ga Yuli, 2025, a gidan Hon. Safana da ke cikin garin Katsina, inda aka bai wa mutane kuɗin hidimar salla tare da bai wa kowace mazaba goma da ke ƙaramar hukumar Safana kuɗi ₦30,000.

Yayin da yake jawabi ga jama’ar da suka halarta, Hon. Safana wanda ke matsayin mai ba Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, shawara kan ayyuka na musamman, ya bayyana cewa an gudanar da taron ne domin ƙara kusanci da juna da kuma tallafa wa jama'a da dan abin sayen naman miya domin shagulgulan Sallah.

“Mun gayyace ku domin mu tattauna, mu ƙara fahimtar juna, da kuma mika tallafin da zai taimaka muku ku samu sauƙin yin bukin Sallah,” in ji shi.

Ya kara da cewa, wannan taimako ba na shi kaɗai ba ne, haɗin gwiwa ne da tsohon kwamishina kuma tsohon ɗan majalisa Hon. Abdulkadir Zakka. Ya ce, “Mun shirya wannan ganawar ne duba da cewa lokaci ya ja ba a zauna irin wannan tattaunawa ba. Mun gayyace ku domin jin ƙorafe-ƙorafinku da ra’ayoyinku, ta yadda za mu fahimci matsalolinku kuma mu nemi hanyoyin magance su.”

Taron ya samu halartar shugabanni da mambobin jam’iyyun APC da PDP, lamarin da ke nuna haɗin kai da fahimta tsakanin al’umma da shugabanninsu. Hon. Safana ya bayyana cewa, halartar mambobin jam’iyyu daban-daban na nuna amincewarsu da irin salon shugabancin da jam’iyyar APC ke gudanarwa. Haka kuma, kungiyar Garkuwa Loyalist da sama da mutum 100 da suka zo karkashin jagorancin Hon. Abdulkadir Zakka, sun halarci taron domin ci gaba da tattaunawa da shugabanni.

A wata hira ta musamman da Katsina Times, Hon. Safana ya bayyana damuwarsa dangane da kalubalen tsaro da ke fuskantar jihar da ƙasa baki ɗaya, inda ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ƙara karfafa gwamnonin jihohi da kayan aiki domin yaki da matsalar tsaro.

“Mun kai shekaru biyu a cikin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dikko Umar Radda, kuma da gaske akwai bangarori da dama da ke bukatar gyara musamman a fannin tsaro. Gwamnan Katsina yana ƙoƙari, amma matsalar tsaro ta addabi al’umma sosai saboda sabbin salo da ‘yan ta’adda ke fito da su. Saboda haka, ina kira ga shugaban ƙasa da ya kara wa gwamnonin ƙarfi da kayan aiki domin su iya shawo kan matsalar tsaro,” in ji Safana.

A nasa jawabin, tsohon kwamishina Hon. Abdulkadir Zakka ya jaddada cewa sun taru ne domin tabbatar wa al’umma cewa tafiyar siyasa na ci gaba karkashin jagorancin Gwamna Dikko da Shugaba Tinubu. Ya bayyana cewa, “A duk fadin Najeriya, jihar Katsina ce shugaban kasa Bola Tinubu ya roƙi a ba ‘yan majalisar da suka koma APC daga PDP tikitin takara kai tsaye, kuma an basu. A yankinmu, ni ne zan jagoranci yakin neman zaben Hon. Ali Iliyasu wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP a zaben 2027.”

Taimakon da gidauniyar Garkuwa ta bayar ya samu karɓuwa daga al’umma, musamman a wannan lokaci da matsin tattalin arziki ya shafi shirye-shiryen bukukuwan Sallah a fannoni da dama.

Follow Us