Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar
Katsina Times | 2 ga Yuni, 2025
Gwamnatin Jihar Katsina ta fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi domin tsara sabbin dokoki da ka’idoji da za su inganta harkokin gudanar da makarantun masu zaman kansu da na al’umma a fadin jihar.
Taron farko kan batun ya gudana ne a ranar Litinin, 2 ga Yuni, a dakin taro na Bello Kofar Bai da ke cikin Sakatariyar Gwamnatin Jihar, karkashin jagorancin Ma’aikatar Ilimi ta Firamare da Sakandare. Ya samu halartar masu makarantu, malamai, shugabannin al’umma da masu fafutukar ilimi.
A jawabinta, Kwamishinar Ilimi ta Firamare da Sakandare, Hajiya Zainab Musa Musawa, ta bayyana cewa hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki zai taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da fannin ilimi gaba.
“Dukkan ku kuna da rawar da kuke takawa wajen gina makomar ‘ya’yan mu. Wannan haduwa alama ce ta hadin kai don dorewar ingantaccen ilimi a Jihar Katsina,” in ji ta.
Kwamishinar ta ce sabbin ka’idojin da ake kokarin kafa suna da nufin samar da tsarin gudanarwa na gaskiya, nagarta da shigar kowa da kowa cikin tafiyar, musamman don bunkasa makarantun al’umma da masu zaman kansu. Dokokin sun samo asali ne daga Manhajar Kasa da ta shafi makarantun da ba na gwamnati ba, da kuma bukatun musamman na jihar Katsina.
Ta bayyana cewa tsarin ya kasu kashi uku:
1. Ka’idojin Gabaɗaya: Sun shafi dukkan matakai daga yara kanana zuwa sakandare, da kuma makarantun sana’o’i da na kwana. Sun kunshi abubuwa kamar aiwatar da manhaja, shugabanci, kula da muhalli, kariyar yara da shigar da masu bukatu na musamman.
2. Ka’idoji Ga Makarantun Masu Zaman Kansu: Wadanda ke fayyace sharudda da hanyoyin kafa da gudanar da irin wadannan makarantu.
3. Ka’idoji Ga Makarantun Al’umma: Wadanda suka fi karkata kan hadin gwiwa da al’umma, da ci gaban makarantun cikin tsari da dorewa.
Hajiya Musawa ta jaddada cewa dokokin ba su zo ne don takura ba, sai dai don inganta ingancin ilimi da kare dalibai daga rashin samun karatu mai ma’ana. Ta ce za a daina bayar da lasisi ga makarantun da ba su cika ka’idoji ba.
“Wannan tsari ba don takura ba ne, illa don kare hakkin dalibai da iyayensu daga karatu maras inganci. Dole ne a cika sharuddan da aka gindaya kafin sabuwar shekarar karatu,” in ji ta.
Ta kara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da sa ido wajen tabbatar da cewa duk wani mai bada ilimi yana aiki bisa tsarin gwamnati, ba tare da katsalandan ko son rai ba.
A cewarta, ka’idojin har yanzu suna matakin farko, kuma ana buƙatar shawarwari da gyare-gyare daga masu ruwa da tsaki domin inganta su. “Gwamnati na buɗe domin karɓar duk wata shawara da za ta tallafa wa wannan tsari,” ta jaddada.
Kwamishinar ta kuma bayyana cewa gwamnati na nazarin amfani da fasahar zamani irin su fasahar wucin-gadi (AI) da shirye-shiryen e-learning, musamman a yankunan karkara, don tallafa wa tsarin karatu da samun damar ilimi ga kowa.
Farfesa Kabir Matazu, daya daga cikin mahalarta taron, ya bayyana cewa da dama daga cikin makarantun al’umma da na masu zaman kansu na aiki ba tare da cikakken tsari ba, wanda hakan ke hana su bin ingantaccen tsarin gwamnati.
“Wannan dama ce ta hada kai da daidaita tafiyar ilimi tsakanin gwamnati da masu bada ilimi,” in ji shi.
An bayyana cewa wani kwamiti na musamman karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar, wanda ya kunshi tsofaffi da sabbin kwamishinonin ilimi, ya gudanar da nazari da gyare-gyare kan tsarin domin tabbatar da cewa yana tafiya da burin gwamnati a fannin ilimi.
A karshe, Ma’aikatar Ilimi ta Firamare da Sakandare ta tabbatar da cewa za ta ba da horo da kayan aiki ga masu makarantu, tare da bukatar hadin kai da bin doka don samar da ingantaccen yanayin karatu da ya dace da bukatun zamani.