Bayan cece-kuce da zanga-zanga; An tono gawar mawaki Mohbad da ake zargin akwai badakala cikin mutuwarsa
![top-news](https://katsinatimes.com/uploads/images/newsimages/KatsinaTimes21092023_143111_FB_IMG_1695306441953.jpg)
- Katsina City News
- 21 Sep, 2023
- 829
"Ƴan sanda a jihar Legas da ke Najeriya sun kammala tono gawar wani fitaccen mawaƙi a ƙasar, Ilerioluwa Aloba da aka fi sani da Mohbad, wanda ya mutu a makon da ya gabata, domin gudanar da binciken musabbabin mutuwarsa.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana haka cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
"An kammala tono gawar, yanzu za a fara gwaji don gano musabbabin mutuwarsa", kamar yadda ya wallafa.
Mawaƙin mai shekara 27, ya mutu ne ranar Talata 12 ga watan Satumba a wani asibiti a Legas, sai dai ba a bayyana abin da ya yi sanadin mutuwarsa ba.
Tun bayan mutuwar tasa, magoya bayansa a biranen kudancin Najeriya suka riƙa yin kiraye-kirayen yi masa adalci, musamman a shafukan sada zumunta.
Hukumomi a jihar Legas sun alƙawarta gudanar da bincike domin gano abin da ya yi sanadin mutuwarsa, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito"