Gwamnatin Katsina Ta Yi Kira Ga Al’umma Su Kare Muhalli da Taimaka Wajen Inganta Tsaro — Inji Abdullahi Garba Faskari

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes07062025_153533_FB_IMG_1749310427700.jpg



Daga Wakilinmu, Katsina TIMES 

Gwamnatin Jihar Katsina ta bukaci al’ummar jihar da su kara himma wajen kare muhalli, gujewa barna ga gandun daji da kuma taimakawa jami’an tsaro da sahihan bayanai domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar 7 ga Yuni, 2025, yayin da ya wakilci Gwamna Malam Dikko Umar Radda, PhD, CON, a wajen bikin hawan Sallar Eid el-Kabir da aka gudanar a Katsina.

A cikin jawabin nasa, Faskari ya taya daukacin al’ummar jihar murnar zagayowar wannan babbar rana ta Eid el-Kabir, yana mai bayyana cewa salla babba na tunatar da al’umma muhimmancin biyayya, hadin kai, da sadaukarwa, kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) da dansa Isma’il (AS) suka nuna a tarihi.

 "Mu yi koyi da Annabi Ibrahim ta hanyar karfafa zaman lafiya, zumunci da hadin kai a tsakaninmu, musamman a irin wannan lokaci na kalubale da duniya ke ciki," in ji shi.

Sakataren Gwamnatin ya jaddada bukatar tsaftar muhalli, musamman ganin cewa damina ta fara sauka. Ya bukaci jama’a da su tabbatar da share magudanan ruwa da gujewa zubar da tarkace a hanyoyin ruwa domin kaucewa ambaliya da yaduwar cututtuka.

Ya bayyana damuwar gwamnatin jihar dangane da yadda ake ci da sare gandun daji ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa hakan yana kara ta’azzarar matsalolin tsaro a yankunan karkara.

 "Gwamnati ta kara wa Kwamitin Aiki da Cikawa karfi domin dakile wannan matsala, kuma an kafa kotu ta musamman da za ta hukunta masu laifi ba tare da bata lokaci ba," in ji Faskari.

Faskari ya bayyana damuwa kan yadda shaye-shayen miyagun kwayoyi ke barazana ga rayuwar matasa, yana mai kira ga iyaye, malamai da shugabannin al’umma da su tashi tsaye wajen wayar da kai da fadakarwa don kare makomar samari da ‘yan mata.

Ya yaba da namijin kokarin da jami’an tsaro ke yi wajen tabbatar da tsaro a fadin jihar, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar na goyon bayansu dari bisa dari. Har ila yau, ya mika sakon taya murna da fatan alheri ga mahajjatan jihar da ke cikin kasa mai tsarki ta Saudiyya, yana addu’ar Allah ya karbi ibadunsu tare da dawo da su gida lafiya.

Gwamnatin Jihar Katsina, a cewar Faskari, za ta ci gaba da aiwatar da muhimman ayyuka a fannonin ilimi, lafiya, noma, gine-gine da ci gaban matasa. Ya bayyana cewa gwamnatin Malam Dikko Radda na da cikakken kudiri wajen inganta rayuwar jama’a da kawo sauyi mai ma’ana.

A karshe, Faskari ya roki al’umma da su gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana da kwanciyar hankali, tare da taimaka wa marasa galihu da karfafa dangantaka a tsakanin juna. Ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya da albarkar damina a fadin jihar da kasa baki daya.

"Allah Ya karbi ibadunmu, Ya albarkaci rayuwarmu da jiharmu, kuma Ya ba mu zaman lafiya mai dorewa," in ji shi.

Follow Us