MATA TA YI YUNKURIN KASHE MIJINTA DA WUKA A KATSINA – Wanda Abin Ya Shafa

Daga Mu'azu Hassan, Katsina TimesWani magidanci mai suna Jamilu Ibrahim Gyaza ya bayyana wa Katsina Times yadda matarsa, Sa'adiyya Lawal Dan Salah, 'yar kimanin shekara 23 daga Funtua, ta yi…

Katsina City News June 30, 2026  ·  12:00 AM
| 164 Views
MATA TA YI YUNKURIN KASHE MIJINTA DA WUKA A KATSINA – Wanda Abin Ya Shafa
MATA TA YI YUNKURIN KASHE MIJINTA DA WUKA A KATSINA – Wanda Abin Ya Shafa

Daga Mu'azu Hassan, Katsina Times



Wani magidanci mai suna Jamilu Ibrahim Gyaza ya bayyana wa Katsina Times yadda matarsa, Sa'adiyya Lawal Dan Salah, 'yar kimanin shekara 23 daga Funtua, ta yi yunkurin kashe shi da wuka a daren Litinin, 29 ga Yunin 2026.

Ma'auratan na zaune ne a yankin Sabuwar Unguwa, kusa da Makarantar Keyway da ke birnin Katsina.

Jamilu ya shaida wa jaridar cewa sun shafe watanni hudu da wasu kwanaki da yin aure. A cewarsa, tun bayan auren ya fara lura da wasu halaye na matarsa da suka sanya ya kwace wayarta har ma ya fasa ta.

Ya ce kwanaki kadan kafin faruwar lamarin, Sa'adiyya ta rika yi masa tambayoyi da suka shafi dukiyarsa, ciki har da kimar gidansa, abin da zai bari idan ya mutu, kudin sallamar aikinsa da sauran kadarorinsa.

Advertisement

A cewarsa, saboda ba ta da waya, yakan ba ta wayarsa domin ta kira 'yan uwanta ko wasu na kusa da ita. Ya ce a ranar Lahadi ta ga an turo masa makudan kudade ta wayar, lamarin da ya sa ta fara tambayarsa lambar sirrin katin cire kudinsa na ATM.


Jamilu ya ce a daren da lamarin ya faru ya lura matarsa ta tanadi wani babban mayafi, amma bai yi zargin komai ba. Ya ce yana kwance a dakinsa ne sai ta shigo ta ce ya gyara yadda yake kwance kamar yadda addini ya tanada. Bayan ya gyara kwanciyarsa ya fuskanci gabas, ya ce yana tsakanin barci da farkawa ne sai kawai ya ji an daba masa wuka a wuya.

"Nan take na fasa ihu, inda 'ya'yana suka ji suka ruga cikin dakin. Duk da haka ta ci gaba da kokarin caka min wuka. Da ta ga ban mutu ba kuma mutane sun iso, sai ta yar da wukar ta durkusa tana kuka tare da rokon gafara, tana cewa ba ta san abin da ta aikata ba, aljanu ne suka rinjaye ta," in ji shi.

Ya kara da cewa daga nan aka kai su Ofishin 'Yan Sanda da ke kusa da Tashar Mota ta Katsina, inda jami'an suka dauki bayanansu da hotunan lamarin. Daga bisani aka garzaya da shi asibiti domin kula da lafiyarsa, yayin da aka tsare matar domin ci gaba da bincike.

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai a ranar Talata, 30 ga Yuni, 2026.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken abin da ya haddasa lamarin kafin daukar matakin shari'a da ya dace.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 2 + 2?