NA ZIYARCI HUBBARE MAFI GIRMA A DUNIYA,MASHAD IRAN.
- Katsina City News
- 02 Oct, 2023
- 997
@ katsina Times
@ jaridar Taskar Labarai.
Birnin Mashad a kasar Iran yana daga cikin birane masu tsohon tarihi a musulunci.
Daga nan wasu sarakunan musulunci sukayi mulki,cikin su har da Mamun da Haruna Rashid.
Marubuta da matafiya na shekarun baya irinsu Ibn Batuta a shekarar 1333 da ibn Khaldun duk sun yi rubutu akan birnin da kuma Hubbaren Imam Musa Ar Ridha( a.s).
A birnin nan ne keda Hubbare Mafi girma a duniyar Musulmi.
Hubbaren kabarin Imam Musa Ar Ridhah ( a.s) ne jika na Manzon Allah, tsatson sayyadah Fatima(as) da sayyadina Ali(a.s)
Hubbare ce dake da Girman daukar mutane Milyan uku a lokaci guda.
Tana da ma aikata dubu tamanin, Da massalatan salloli biyar 27, da massalacin jumma a 12, da katafaren dakin karatu Wanda yana cikin manyan dakin karatu a yankin gabas ta tsakiya, yana da makarantun koyon Addini guda 20, Asibiti dakin shan magani da wurin cin abinci.
Hubbaren yana da katafaren sayar da litattafai da kuma buga su, Duniya guda ce.
Manyan manyan masaukan baki ke kewaye da Hubbaren.
Maziyarta na zuwa daga koina a Duniya har da wadanda ba musulmi ba.
Na hadu da wani dan kasar faransa da yace yazo ne yayi ilmi akan yadda aka Gina Hubbaren ake kuma kula dashi
Mutumin masanin gine gine ne,cewa yayi tsarin ginin na cikin gine ginen da ake nazarinsu a kasashen Duniya.
Akwai karkashin kasa mai daukar kusan mutane Milyan daya , akwai sama.
In kai kuskuren bacewa a cikin Hubbaren, addu a ce kawai zata fitar da kai.
Mutanen Iran basu Jin turanci, Malaman su kadai ke jin larabci.Don haka sai addu a ar Allah, ya hada ka da bako da zai fahimce ka.
Suna da wajen da Zaka je in ka bace nan akwai masu jin yare, Kala kala, amma gano ofis din tashin hankali ne
www.katsintimes.con
www.jaridartaskarlabarai.com
All in All social media platforms