Tumaki Sun Cinye Ganyen Wiwi Kilo 272 Sun Yi Ta Tsalle
- Katsina City News
- 01 Oct, 2023
- 993
Aminiya
Wani ayarin tumaki ya fada a wata gonar gwaji (Green House) a kasar Girka inda tumakin suka cinye ganyen tabar wiwi mai nauyin kilo 272.155 da aka shuka domin yin magani da ita.
Kafar labarai ta UPI ta ruwaito a ranar Litinin da ta gabata cewa mamallakin gonar mai suna Yiannis Bourounis da ke zaune a garin Magnesiya ya ce shukar ta hadu da matsala sakamakon zafi da kuma ambaliyar da aka yi kwanan nan, lokacin da tumakin suka shiga gonar suka yi dabdala da sauran ganyen wiwi din.
Ya yi kiyasin tumakin sun lamushe fiye da kilo 272 na wiwin.
Bourounis ya shaida wa kafar labarai ta thenewspaper.gr cewa tumakin sun rika tsalle fiye da yadda aka saba ganin awaki na yi bayan sun cinye ganyen wiwi din.
Kasar Girka dai ta halatta yin amfani da ganye wiwi wajen yin magani a shekarar 2017, kuma kasar ta bude kamfanin sarrafa wiwi na farko a farkon bana.