Shugaba Tinubu ya yi wa ma'aikatan Najeriya karin albashi na wucin gadi.
- Katsina City News
- 01 Oct, 2023
- 865
Daga Janaidu Amadu Doro
Shugaban ya sanar da hakan ne a jawabinsa ga ’yan Najeriya na cikar kasar shekakara 63 da samun ’yancin kai da safiyar yau Lahadi.
A cewarsa karin Albashin wucin Gadin an yi shi ne don rage radadin cire tallafin mai da ya shafi ma'aikatan kasar Nan da sauran Al'umma.
Ya Kara da cewar matsakaicin ma’aikaci zai samu karin Naira Dubu Ashirin da biyar N25,000 a kan albashinsa a cikin wata shida masu zuwa, To amma shugaban bai bayyana lokacin da za a fara biyan karin albashin ba.
Ya bayyana cewa ya na sane da irin wahalar da al’ummar kasar nan su ka shiga a sakamakon cire tallafin man da aka yi, amma duk da haka dole sai an yi hakuri da hakan, muddin ana so kasar ta samu ci gaban da ake bukata.