Sarkin Musulmi Ya Ayana Juma’a a Matsayin Ranar Sallah Karama

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes18032026_200002_FB_IMG_1773863945829.jpg



KatsinaTimes 18 Maris 2026

Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Addini na Majalisar Masarautar Sakkwato tare da hadin gwiwar Kwamitin Ganin Watan Ƙasa sun sanar da cewa ba su samu rahoton ganin sabon watan Shawwal 1447AH daga sassan ƙasar nan ba.

A wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, 18 ga Maris, 2026, kwamitin ya bayyana cewa ranar ta kasance rana ta 29 ga watan Ramadan 1447AH. Don haka, an ayyana ranar Alhamis, 19 ga Maris, 2026 a matsayin cika kwanaki 30 na watan Ramadan.

Bayan karɓar rahoton, Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Muhammad Sa’ad Abubakar, ya amince da sakamakon tare da ayyana ranar Juma’a, 20 ga Maris, 2026 a matsayin ranar 1 ga watan Shawwal 1447AH, wadda za a gudanar da Sallar Idi (Eid-el-Fitr).

Sarkin Musulmi ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin Ramadan, tare da yi musu fatan samun shiriya da albarkar Allah. Haka kuma ya bukace su da su ci gaba da addu’a domin zaman lafiya, hadin kai da ci gaban ƙasa, yana mai yi wa kowa fatan murnar Sallah cikin farin ciki da kwanciyar hankali.

Follow Us