Harin ‘Yan Bindiga Ya Sa Mazauna Kigwali a Kaduna Sun Tsere Daga Gidajensu

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes16032026_123638_FB_IMG_1773664596395.jpg



KatsinaTimes 

Mazauna ƙauyen Kigwali da ke ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna sun tsere daga gidajensu bayan wani hari da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai a yankin.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:50 na safiyar ranar Asabar, lokacin da wasu gungun ‘yan bindiga masu ɗauke da bindigogi kirar AK-47 suka kutsa cikin ƙauyen tare da harbe-harbe domin tsoratar da mazauna yankin.

Wani mazaunin ƙauyen, Samaila Yakubu, ya ce maharan sun riƙa harbi a iska bayan sun shiga ƙauyen, lamarin da ya sa jama’a suka tsere zuwa cikin daji domin tsira da rayukansu.

A yayin harin, wani mazaunin ƙauyen mai suna Isah Sabo ya samu munanan raunuka bayan harbin bindiga ya same shi. Yakubu ya bayyana cewa Sabo ya samu harbin ne a kafaɗa lokacin da yake ƙoƙarin tserewa ta taga daga ɗakinsa.

Ya ƙara da cewa bayan harbin, maharan sun kuma daba masa adda a hannuwansa biyu suka bar shi cikin mawuyacin hali.

“Duk da haka, daga bisani ya samu ƙarfin guiwa ya yi tafiya zuwa ƙauyen Allewa, daga inda aka garzaya da shi asibiti a Katari domin samun kulawar likitoci,” in ji Yakubu.

Wani jagoran al’umma a yankin, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar harin tare da bayyana cewa ƙauyen Kigwali yanzu ya kusan zama babu kowa saboda mazauna yankin sun tsere.

Ya ce mutanen da suka bar gidajensu suna samun mafaka ne a ƙauyen Azara da ke makwabtaka da su.

Jagoran ya nuna damuwa kan yadda hare-haren ‘yan bindiga ke ƙaruwa a yankin, yana mai cewa ƙauyuka da dama a yankin sun riga sun zama kufai saboda hare-haren da ake yawan kaiwa.

Wata majiya ta tsaro, wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ta tabbatar da cewa dakarun tsaro sun isa yankin daga bisani inda suka fatattaki maharan.

Majiyar ta kuma tabbatar da cewa mutum guda ne ya samu raunin harbin bindiga a harin.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, kakakin rundunar 'yansanda a jihar Kaduna, Mansur Hassan, bai fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Follow Us