Fatan Malaman Makarantun Firamare Ga Gwamnan Katsina A Shekarar 2026

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes10012026_233353_FB_IMG_1768087967177.jpg

Daga Wakilanmu
Katsina Times

A ƙarshen shekarar 2025, malaman makarantun Firamare a jihar Katsina sun bayyana wani babban fata ga Gwamnan jihar Katsina, inda suka roƙi Allah Ya ba shi ikon aiwatar da cikakkiyar dokar Gwamnatin Tarayya da ta shafi Malamai.

Dokar, wadda aka amince da ita a zamanin marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ta tanadi cewa Malami zai iya ci gaba da aikin koyarwa har ya kai shekaru 65, ko kuma ya cika shekaru 40 yana aiki a fannin malanta kafin ya yi ritaya. 

Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da dokar a matakin ƙasa, tare da barin jihohi masu buƙata su aiwatar da ita.

Malaman sun bayyana cewa wasu jihohi sun riga sun tabbatar da dokar domin ci gaban ɗorewar Malamai ƙwararru, musamman a makarantun Firamare da ke koyar da yara ƙanana. 

Sun ƙara da cewa wasu jihohi na kan aiwatar da dokar, ciki har da jihar Katsina.

A cewarsu, Gwamnan Katsina, wanda tsohon Malami ne, kuma mai kishin ilimi da karatu, na da cikakken fahimta game da muhimmancin wannan doka ga inganta tsarin ilimi.

Malaman makarantun sun bayyana fatansu na ganin aiwatar da dokar a matsayin zaɓi, inda duk malamin da yake so zai iya ci gaba da aiki har ya kai shekaru 65, ko kuma ya cika shekaru 40 yana koyarwa.

Sun jaddada cewa aiwatar da wannan doka zai taimaka wajen ƙara inganci da ƙwarewar Malamai, tare da inganta koyarwa a makarantun Firamare na jihar.

Wannan yana daga cikin manyan buƙatu Malaman makarantun jihar Katsina da suke fatan cimmawa a shekarar 2026.

Follow Us