NDLEA Katsina Ta Kama Mutune 1,018, Ta Kwace Miyagun Ƙwayoyi Sama da Kilo 2,400 a Shekarar 2025.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes06012026_173525_FB_IMG_1767720885034.jpg


Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) a Jihar Katsina, ta bayyana cewar ta samu gagarumar nasara a yaƙin da take yi da shan miyagun ƙwayoyi da safararsu a shekarar 2025, inda ta kama mutum 1,018 tare da kwace miyagun ƙwayoyi masu nauyin sama da kilo 2,400.

Kwamandan hukumar na Jihar Katsina, CN Samaila Danmalam, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai na ƙarshen shekarar 2025 da hukumar ta kira 'ya jarida ciki har da Katsina Times, wanda aka gudanar a ranar Talatar nan 6 ga Janairu, 2026, a hedikwatar hukumar da ke Katsina.

A cewarsa, nasarorin da aka samu sun biyo bayan dabarun aiki guda biyu da hukumar ta NDLEA ke amfani da su a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar na kasa, Birgediya Janar Muhammed Buba Marwa (Rtd), wato dakile samar da miyagun ƙwayoyi da kuma rage yaduwarsu a tsakanin al’umma.

Ya ce, “a shekarar 2025, jami’an NDLEA sun gudanar da samame bisa sahihan bayanan sirri da sintiri a sassa daban-daban na jihar, lamarin da ya haifar da tarwatsa hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi.”

"Daga cikin adadin mutanen da aka kama, an kama maza 992 mata kuma 26, jimillar mutane 1,018 ke nan." In ji Danmalam

Ya ci gaba da cewar, "NDLEA ta samu nasarar kwace nauo'in kwayoyi daban-daban", yana mai bayyana miyakun kwayoyin da suka hada da: Cannabis kilo 1,667.747, Codeine kilo 12.348, da kuma psychotropic kilo 793.66, wanda ya kai jimillar kilo 2,473.755 a misali.

Harwayau, Kwamandan ya kuma bayyana cewar shirin farmaki na mai taken "War Against Drug Abuse (WADA)" ya taka muhimmiyar rawa wajen rage shan miyagun ƙwayoyi a jihar; "an gudanar da shirye-shiryen wayar da kai guda 203, inda mutane 75,135 suka amfana. Haka kuma, an ba mutane 451 shawarwari na musamman, yayin da aka shigar da mutane 58 cibiyoyin gyaran hali na masu shan miyagun ƙwayoyi." In ji shi

Bugu da kari, Danmalam ya bayyana wa manema labarai cewar, a bangaren shari’a, hukumar a matakin jiha, ta gurfanar da mutane 86 a gaban kotu, yayin da aka samu hukunce-hukuncen shari’a har guda 87 a kan masu laifi.

Sai dai kuma, Danmalam ya koka tare da bayyana irin ƙalubalen da hukumar ke fuskanta, yana mai bayyana kayan aiki, musamman ƙarancin motocin aiki, gine-ginen ofis da masaukin jami’ai a faɗin jihar a matsayin abin da ke ci masu tuwo a kwarya.

"NDLEA na kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su bada gudummawa domin shawo kan matsalolin." Ya yi kira.

Da yake karkare jawabin nasa, CN Samaila Danmalam ya yi jinjina ga Shugaban humar NDLEA na ƙasa, Birgediya Janar Muhammed Buba Marwa (Rtd), bisa irin sauye-sauyen da ya kawo a hukumar, tare da taya shi murnar sake naɗa shi da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi.

Haka kuma, ya yi godiya da yaba wa Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda bisa tallafin da take bai wa hukumar, musamman na gyaran motocin aiki da ɗaukar nauyin shirye-shiryen gyara halayen masu ta'ammuli da shan ƙwayoyi, yana mai addu'ar lafiya da tsayin kwana ga iyayen kasa, sarakunan Katsina da Daura bisa shawarwari da haɗin gwiwar da suke yi da su. Ya kuma gode wa rundunonin tsaro, bisa taimako da haɗin gwiwa da suke yi, yana mai shan alwashin kara kaimin gudanar da aikinsu da saurarn rukunin jam'ian tsaro ba da gajiyawa ba.

"NDLEA na tabbatar wa al’ummar Jihar Katsina cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da safararsu, tare da kira ga jama’a da su bayar da haɗin kai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’umma a jihar." Ya jaddada.

Daga karshe, Kwamandan ya bayyana cewa hukumar ta NDLEA ta ɗaga matsayin jami’anta guda 61 a matakai daban-daban, ciki har da sauya wasu daga Non-Commissioned Officers zuwa Commissioned Officers, inda aka ɗaga jami’ai biyar daga matakin One star zuwa Two star, tare da ɗaga wasu jami’ai 56 zuwa mukamai daban-daban.

Follow Us