Babbar Kotun Jihar Katsina Ta Horar da Alƙalai (Magistrates) kan ICT, AI da Sabbin Kafofin Watsa Labarai

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes06012026_150016_FB_IMG_1767711531001.jpg


Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, 6 ga Janairu, 2026

Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Katsina a ranar Talata ta shirya taron horaswa na musamman ga alƙalan majistire domin ƙarfafa harkar shari’a a Zamani, mai taken “Ƙarfafa Ƙwarewa kan ICT tare da Mai da Hankali kan Basirar Wucin-Gadi (Artificial Intelligence – AI) da Sabbin Kafofin Watsa Labarai.”

An gudanar da taron ne a dakin taro na Babbar Kotun Shari’a ta Jihar Katsina, inda Gwamnatin Jihar Katsina ta shirya hadin gwiwa da kamfanin Matasa Media Links, mamallakin Jaridar Katsina Times, Katsina City News magazine da jaridar taskar labarai.

A jawabin buɗe taro, Alkalin Alkalai na Jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar, ya bayyana cewa fasaha ta zama wani muhimmin ɓangare na rayuwar ɗan Adam, kuma ba za a iya raba ta da tsarin shari’a na zamani ba.

Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar ya gabatar da jawabinsa ta hanyar na’ura (digital), domin dacewa da taken taron, inda ya ce taken jawabinsa “Sabuwar Hanya zuwa Adalci ta Hanyar Kotuna Masu Amfani da Fasaha” na nuna yadda fasaha ta zama ginshiƙi wajen saurin gudanar da shari’a, gaskiya da sauƙaƙe ayyukan kotuna.

“Shekaru talatin da suka gabata, amfani da fasaha a kotuna abu ne da ba a ma tunaninsa. A yau kuwa, ICT ta zama hanya ta inganta gudanar da shari’a,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, a da kotuna na dogaro ne da rubuce-rubuce da bayanan hannu kawai, amma a yau fasaha na taka muhimmiyar rawa wajen adana bayanai, sadarwa, gudanar da shari’a da kuma bai wa al’umma damar samun adalci cikin sauƙi.

Da yake jawabi a madadin masu shirya taron, Ahmed Abdulkadir, Darakta a Matasa Media Links, ya ce an tsara taron ne domin nunawa wa alƙalan majistire fahimta mai zurfi kan tasirin basirar wucin-gadi (AI) da sabbin kafofin watsa labarai a harkar shari’a.

“AI da sabbin kafofin watsa labarai ba wai sabbin abubuwa ba ne kawai, sun zama wata rayuwa ta yau da kullum,” in ji shi. “AI na iya ƙirƙirar rubutu, hotuna, sauti da bidiyo da za su yi kama da na gaske, lamarin da ke haifar da tambayoyi masu muhimmanci kan hujja, sahihanci, sirri da alhaki a gaban kotuna.”

Ya bayyana cewa manufar taron ba wai juyar da alƙalai zuwa ƙwararrun masana fasaha ba ne, sai dai don gina fahimta, ƙwarin gwiwa da hikimar yanke hukunci a shari’o’in da suka shafi fasaha da kafofin sadarwa.

Taron ya samu halartar ƙwararrun malamai da masana, ciki har da Farfesa Mainasara Yakubu Kurfi daga Sashen ilimin aikin jarida (Mass Communication) na Jami’ar Bayero, Kano.

Farfesa Kurfi ya gabatar da takarda mai taken “Shari’a a Zamanin Kafofin Sadarwar Zamani: Ka’idoji, Ayyuka da Mafi Kyawun Dabi’u ga Alƙalan Majistire na Jihar Katsina,” inda ya yi bayani kan yadda alƙalai za su yi amfani da kafofin sada zumunta cikin ladabi da ƙa’ida, tare da kiyaye mutuncin ofishinsu.

Tun da farko a nata jawabin maraba, Babbar Magatakardar Kotun ta Jihar Katsina, Hajiya Basira, ta nuna godiya ga Alkalin Alkalai bisa amincewa da shirya taron, tare da yabawa alƙalan majistire bisa jajircewarsu wajen ƙara ilimi da ƙwarewa.

Ta bayyana taron a matsayin muhimmin shiri na ilimi da zai ƙarfafa kotuna da inganta aikin shari’a a jihar.

Maharta taron sun bayyana farin cikinsu da irin ilimin da suka samu, tare da jaddada cewa horon zai taimaka musu wajen fuskantar ƙalubalen shari’o’in da suka shafi fasaha da sabbin kafofin watsa labarai.

Taron ya ƙara nuna kudirin babbar Kotun Shari’a ta Jihar Katsina na ci gaba da gina ƙwarewar alƙalai, amfani da fasaha cikin gaskiya, da kuma shirye-shiryen tunkarar ƙalubalen shari’a a zamanin basirar wucin-gadi da kafofin sadarwa na zamani.

Follow Us