Fafaroma Francis ya yi kiran a sasanta rikicin Nijar cikin lumana
- Katsina City News
- 20 Aug, 2023
- 903
Fafaroma Francis ya yi kiran a sasanta rikicin siyasar Nijar ta laluma biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yuli.
"Ina lura cikin damuwa da abin da ke faruwa a Nijar," a cewarsa yayin da yake jawabi yayin ibada a Dandalin St Peter's a yau Lahadi.
"Na bi sawun bishop-bishop wajen neman zaman lafiya a ƙasar da kuma yankin Sahel.
"Ina taya ƙasashen duniya da addu'a a yunƙurinsu na lalubo bakin tsaren cikin kwanciyar hankali don zaman lafiyar kowa da kowa."
Ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma, Ecowas, ta yi barazanar yin amfani da ƙarfin soja wajen tilasta wa sojojin mulkin mayar da mulki ga farar hula.