KatsinaTimes
Gwamnatin Tarayya ta sanar da haramta bai wa duk wani jami’in gwamnati mai rike da mukami digirin girmamawa, a kokarin da ta ke yi na dakile yawan sabawa ka’ida wajen bayar da irin wadannan digirgir.
Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ce ta bayyana hakan, inda ta ce ta dauki matakin ne bayan samun rahotanni masu tayar da hankali game da yadda ake bayar da digirin girmamawa barkatai da amfani da su ta hanyoyin da ba su dace ba.
Shugaban Hukumar NUC, Farfesa Abdullahi Yusufu Ribadu ne ya bayyana hakan a Abuja, jim kadan bayan karbar rahoton kwamitin bincike kan yadda ake bayarwa da amfani da digirin girmamawa a fadin kasar.
A cewarsa, binciken da NUC ta gudanar ya gano yadda ake ta’ammali da digirin girmamawa ba bisa ka’ida ba, musamman karya dokokin Keffi Declaration na shekara ta 2012, wadda ta tanadi cewa jami’o’i ba su da hurumin ba wa masu rike da mukaman gwamnati irin wadannan digirgir.
Ya ce Dokar ta kuma haramta wa duk mai karbar digirin girmamawa amfani da lakabin “Dr” sai dai a bayyana shi da sunan da ya dace, kamar Doctor of Literature (Honoris Causa).
Farfesa Ribadu ya bayyana cewa wannan ba kawai batun ladabi ko tsarin aiki ba ne, har ila yau yana da nasaba da dokoki, domin amfani da lakabin “Dr” ba tare da cikakken bayani ba na iya zama laifi a karkashin dokokin da suka shafi yaudara a Najeriya.
Ya ce irin wannan almundahana tana rage darajar jami’o’i tare da lalata amincewar jama’a ga sahihan digirgir da ake nema da gumi.
Rahoton kwamitin ya gano cewa akwai cibiyoyi 32 da ke aiki a matsayin “masana’antar digirin girmamawa” a kasar, ciki har da:
Jami’o’i takwas (8) na waje marasa amincewar hukuma
Jami’o’i hudu (4) na cikin gida ba su da lasisi
Kungiyoyi 15 da ba su da ikon bayar da wani digiri
Da wasu cibiyoyi uku (3) da ba su da hurumin bayar da digiri
Wasu daga cikin su ma, a cewar NUC, suna zuwa har matakin bayar da farfesa na jabu.
Farfesa Ribadu ya jaddada cewa doka ta bai wa jami’o’in gwamnati da masu zaman kansu ne kadai ikon bayar da digirin girmamawa, amma bisa kwarewa da bin ka’ida. Ya ce dole ne masu karɓa su yi amfani da irin digirin cikin tsarin sunan da ya dace, ba tare da yin ikirarin kasancewa “Dr” ba.
Ya ce NUC za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace don kare martabar ilimi da tabbatar da bin ka’idojin da suka shafi bayar da digirin girmamawa a Najeriya.