PDP Tsagin Wike Ta Kori Wasu Gwamnoni da Manyan Jiga-jiganta a Zaman NEC

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes18112025_151738_FB_IMG_1763478992959.jpg



KatsinaTimes 

Jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Nyesom Wike ta sanar da korar Gwamnan Oyo, Seyi Makinde; Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed; Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, da fitaccen jigon jam’iyya, Cif Bode George.

Haka nan jam’iyyar ta dakatar da wasu manyan shugabanni, ciki har da tsohon Shugaban Kwamitin Amintattu na PDP (BoT), Sanata Adolphus Wabara; Sanata Kabiru Tanimu Turaki; Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kudu, Taofeek Arapaja; da wasu, bisa zargin gudanar da ayyuka da suka saba wa muradun jam’iyyar.

NEC ta kuma amince da rusa kwamitocin shugabancin jam’iyya na jihohin Bauchi, Oyo, Zamfara, Yobe, Legas, Edo da Ekiti.

An yanke waɗannan hukunci ne a zaman NEC na 103 da aka gudanar a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja, a yau Litinin.

Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP, Alhaji Mohammed Abdulrahman, wanda ya gabatar da rahoton kan wadannan matakai, ya ce an dauki wannan hukunci ne sakamakon raina hukuncin kotu da wasu daga cikin manyan kusoshin jam’iyyar suka yi, lamarin da ya ce ya rage wa PDP ƙima a idon jama’a.

A halin da ake ciki, ana ci gaba da muhawara kan tambayar da ke tasowa a zukatan mambobin jam’iyyar: Su waye ke da cikakken iko kan jam’iyyar – tsagin Wike ko na Bala Mohammed?

Follow Us