Tinubu ya umarci a gaggauta ceto ɗaliban makaranta da aka sace a Kebbi

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes17112025_201206_FB_IMG_1763410298651.jpg


Mohammed Idris, ministan yaɗa labarai, ya ce Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggawa domin ceto dalibai mata da aka sace daga Makarantar Gwamnati ta ’Yan Mata da ke Maga, jihar Kebbi.

’Yan bindiga sun kai farmaki makarantar da safiyar Litinin, inda suka yi garkuwa da dalibai mata 25.

Mai magana da yawun ’yansanda a Kebbi, Nafi’u Kotarkoshi, ya ce Mataimakin Shugaban Makarantar, Hassan Makuku, ya rasa ransa a yayin harin, yayin da Ali Shehu, ɗan banga, ya samu raunuka a hannunsa na dama sakamakon harbin da aka yi masa.

Yayin da yake mayar da martani kan lamarin a cikin wata sanarwa, Idris ya ce Tinubu ya yi Allah-wadai da harin tare da tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kare rayukan ’yan Najeriya, musamman dalibai.

“Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya jaddada cewa kare rayukan ’yan Najeriya, musamman na ɗalibai, babban nauyin Gwamnati ne. Gwamnati ta la’anci wannan mummunan hari kan ɗalibai marasa laifi da kuma kashe jami’an makarantar da ke gudanar da aikinsu na ƙwarai,” in ji shi.

“An bai wa hukumomin tsaro da leken asiri umarni kai tsaye da su gano inda aka kai daliban, su ceto su cikin koshin lafiya, sannan su tabbatar da cewa waɗanda suka aikata wannan aika-aika sun fuskanci hukunci. Gwamnatin Tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an cimma wannan buri.”

“Mun tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ƙarfafa harkar tsaro na ƙasar nan na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin tarayya ta sanya a gaba. Gwamnati na sake fasalin rundunonin soji, ’yan sanda da na leken asiri domin magance hare-hare da kuma hanzarta mayar da martani cikin gaggawq duk lokacin da barazana ta taso.”

“Haka kuma, Najeriya na ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashen yankin ta hannun ECOWAS, Tarayyar Afirka da MNJTF domin tsare iyakoki da dakile ayyukan ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu aikata laifi. Muna kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da nuna kwarin gwiwa yayin da jami’an tsaro ke aiki ba dare ba rana domin warware wannan lamari.”

Follow Us