An kira ga Uwar Jam'iyyar APC ta dauki matakin kan Rabiu Adamu Funtua kan yadda suke shirya Tarukan yi ma APC tawaye a garin Funtua

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes10112025_135558_Screenshot_20251110-145145.jpg

An kira ga Uwar Jam'iyyar APC ta dauki matakin kan Rabiu Adamu Funtua kan yadda suke shirya Tarukan yi ma APC tawaye a garin Funtua 

Wasu magoya bayan jam'iyyar APC a jihar Katsina sun yi kira ga Gwamna Radda da Uwar Jam'iyyar a jihar da ta dauki matakin gaggawa kan Abunda Suka kira da Cin Amana ga jam iyya,  kasancewar shi Alh Rabiu kani ne ga Kwamishinan lafiya,  kuma Wanda yafi kowa Amfana da jam iyyar Apc A Funtua,  Wajen bashi kwangiloli da Taimako da yake samu fiye da ko wane dan jam iyyar A funtua, a ranar Lahadi 9 ga watan Nuwamba 2025. 

A cewarsu, ya shirya taron jama'a a makera ward, don ayi ma Ɗan majalisar na jiha karkashin jam iyyar, APC tawaye tare da yin maganganun da basu dace ba kan wasu masu rike da mukaman siyasa na garin Funtua 

Haka zalika mutanen sun yi zargin yana hurema matasa kunne suna cin mutumcin ya'yan jam'iyyar Apc A Social media, wanda Hakan zagon kasa ne ga jam'iyyar. 

Wanda hakan bārazāna ce ga Jam'iyyar APC a zaben 2027. Dalilin hakan yasa muke kira ga Gwamna Radda da Uwar Jam'iyyar APC ta jiha da ta dauki matakin tsawatarwa ga Rabiu  don samun nasarar APC a zabe mai zuwa.

Wasu daga cikin magoya bayan jam'iyyar APC da suka gabatar da korafin sun haɗa da Mataimakin shugaban kansolili na Funtua,  kuma kansila mai Wakiltar Ung musa Ward,  Hon Gali Sadau, sai kansilan Makera, Hon. Bala Gardawa da kansilan Tudun iya Ward,  Hon. Ismail Ibrahim, Kansilan Goya,  Hon. Surajo Goya  da Wasu daga Cikin masoya jam iyyar Apc Funtua local Government.

Daga ƙarshe, magoya bayan jam'iyyar APCn sun zargi Rabi'u Adamu Funtua da raba kawuwan membobin APC a karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina.

Follow Us