Kungiyar IZALA ta tara kudi Naira miliyan dari da bakwai ta dalilin tattara fatun layya (₦107,704,484.25)
- Katsina City News
- 20 Aug, 2023
- 1089
Ibrahim Baba Suleiman
Kungiyar wa'azin musulunci mai kira a kau da bidi'a a tsaida sunnar Annabi Muhammad mai tsira da aminci, ta tara naira miliyan dari da bakwai da dari bakwai da hudu da naira dari hudu da hudu da kwabo ashirin da biyar (₦107,704,484.25) na tattara fatun layyan da ya gabata na shekarar 1443/2022.
A bana Jihar da tafi ko wace jiha kawo kudi itace jihar Sokoto inda ta tara Naira miliyan goma sha uku da dubu dari takwas da tamanin da shida da naira hamsin kacal (13,886,050,00)
Jihar kaduna ita tayi na biyu inda ta tara fatun Naira miliyan goma sha uku da dubu dari uku da talatin da tara da naira dari shida kacal. (₦13,339,600.00).
Jihar Kebbi ita tayi na uku inda ta tara fatun Naira miliyan goma da dubu dari da sha biyar da naira dari biyu da tamanin kacal. (₦10,115,280,00)
Haka lamarin ya gudana a dukkan jihohin Naijeria talatin da shida harda Abuja.
A cikin bayanan sa shugaban IZALA na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yabawa al'ummar kasar matuka wajen bada hadin kai a wannan aikin tare da tabbatar da gudanar da kudaden kamar yadda yakamata, ya kuma yabawa tare da jinjina ga kwamitin tattara fatun layyan da kwamandojin agaji da suka tura wakilai a ko wace jiha kuma suka jajirce wajen ganin aikin ya gudana yadda ake bukata.
A baya angina katafaren masallaci da gidan shan magani gami da katafaren masaukin baki a cikin birnin Abuja duka da kudaden fatun layyan da jama'a ke badawa.
Allah ya sakawa duk wanda ya sanya jarinsa a wannan aiki da gidan Aljanna. Amin
JIBWIS NIGERIA
media@jibwisnigeria.org