Muhammad Ali Hafizy, Katsina Times. 26 Oktoba 2025
An kammala taron kwanaki biyu na horaswa ga matasa kan harkar kudin intanet da ake kira “Crypto” a cibiyar Katsina Vocational Training Centre (KVC) da ke Katsina.
Taron, wanda aka gudanar a hadin gwiwa tsakanin KVC da Paracha Family Abuja, ya gudana daga ranar Asabar 25 zuwa Lahadi 26 ga watan Oktoba, 2025.
A yayin taron, Malam Abubakar Gwani Salisu daga Jihar Katsina ne ya jagoranci koyarwar, inda ya yi bayani kan yadda kasuwar “Crypto” ke aiki, hanyoyin saye da sayarwa, da kuma matakan kare kai daga matsalolin da ke tattare da harkar.
Daga cikin mahalarta taron akwai matasa daga sassa daban-daban na Jihar Katsina, wadanda suka bayyana jin daɗinsu da yadda aka gudanar da horaswar. Sun ce sun samu sabbin ilimi kan yadda ake cin moriyar kasuwar kudin intanet cikin tsari da kariya.
Sun kuma gode wa masu daukar nauyin taron bisa wannan dama da suka samar domin inganta rayuwar matasa da bunkasa sana’o’in zamani a jihar.