AN HALLAKA DAN TA ADDA MAI SUNA BLACK..A YANKIN BATSARI
- Katsina City News
- 20 Aug, 2023
- 1431
Misbahu Ahmad Batsari
@ katsina times
A ranar litanin 14-08-2023 jami'an tsaro da ake kira special hunters suka kai samame a maboyar wani kasurgumin dan bindiga Wanda ake kira Black a maboyar sa dake yankin yammacin Yangayya a cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Sunyi nasarar hallaka barayin tara (9) ciki hadda kacallan su watau Black kamar yadda wani mazaunin yankin ya bayyana mamu, inda yace a gaban idon su maaikatan suka dawo da babura guda ukku da bindigun barayin guda ukku cikin annashuwa suna murna. Ya Kara da cewa dama wadannan barayin ne suka addabi yankin nasu da kisa garkuwa da mutane da tazarta mata da Kuma yi masu tara ba gaira ba dalili.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai
07043777779 08157777762