Shettima zai halarci taron ƙasa na MSME a Katsina da kaddamar da wasu manyan ayyukan gwamnatin jihar.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes17102025_232054_FB_IMG_1760743169803.jpg

KatsinaTimes 

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, zai ziyarci jihar Katsina a ranar Litinin mai zuwa domin halartar taron ƙasa na matsakaitan masana’antu (MSME Clinic), tare da kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin jihar karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda ta aiwatar.

An bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar Katsina a ranar Juma’a, wanda jaridar Katsina Times ta halarta. Taron ya samu halartar wasu daga cikin mambobin majalisar zartarwa da manyan jami’an gwamnati, karkashin jagorancin Kwamishinan Yaɗa Labarai, Dr. Bala Salisu Zango.

Ziyarar da ke nuna ci gaban tattalin arziki.

A cikin jawabinta, Daraktar Hukumar Ci gaban Kasuwanci ta Katsina (KASEDA), Hajiya Aisha Aminu Malumfashi, ta bayyana ziyarar a matsayin babbar alamar ci gaba ga tattalin arzikin jihar Katsina, musamman wajen ƙarfafa matasa da ‘yankasuwa.

Ta ce taron MSME Clinic na 9, wanda za a gudanar a ranar Talata, 21 ga Oktoba, 2025, zai haɗa daruruwan ‘yankasuwa ƙanana, hukumomin gwamnati da cibiyoyin kuɗi domin nune-nunen kasuwanci, bayar da shawarwari, da tallafi kai tsaye.

“Wannan shiri ba kawai taro ba ne, dama ce ta canja rayuwa ga kananan ‘yankasuwa. Matasa, mata, da masu sana’o’i za su gana da hukumomi kamar BOI, BOA, SMEDAN, NEXIM, da NAFDAC domin yin rijista, neman rance, da samun shawarwari kaitsaye,” in ji ta.

Hajiya Malumfashi ta kuma sanar da cewa za a gudanar da bikin MSME Awards Night na farko a Katsina, inda Mataimakin Shugaban Ƙasa da Gwamna Radda za su karrama ‘yankasuwa masu hazaka da jajircewa, duk da ƙalubalen tattalin arziki.

Kaddamar da sabuwar hanya da Manhajar KASPA Platform.

A nasa jawabin, Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri, Injiniya Kabir Magaji Ingawa, ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa zai kuma kaddamar da sabuwar hanyar kilomita 3.3 mai hannu biyu, daga shataletalen Babban Masallacin Juma’a zuwa shataletalen Kidis ta wuce zuwa shataletalen makarantar 'yanmata ta WTC, a kan kuɗin ₦1.9 biliyan.

Ya ce an gina hanyar da fitilun hasken rana, hanyar masu tafiya a ƙasa, da magudanar ruwa domin ƙara tsaro, rage cunkoso da kuma kyautata kwalliyar birnin.

“Wannan hanya ba kawai aikin gini ba ce, hanya ce ta kasuwanci. Za ta sauƙaƙa zirga-zirga, rage lokaci, da taimaka wa ‘yan kasuwa yin aiki har da daddare,” in ji shi.

A gefe guda, Kwamishinan Noma da Albarkatun Ƙasa, Farfesa Ahmad Muhammad Bakori, ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa zai kuma ƙaddamar da manhajar 'KASPA Digital Agriculture Platform' wani dandali na noma ta fasaha da ke haɗa manoma kaitsaye da masana, kasuwanni, da masu sayar da kayan noma a fadin kananan hukumomin jihar 34.

 “KASPA ginshiƙin sauyi ne da zai ƙara sadarwa a harkar noma, ya haɓaka samar da abinci, da kuma inganta ribar manoma. Tare da wayar salula kaɗai, manomi zai iya samun shawara, sayen iri masu kyau, da sayar da amfanin gona kai tsaye ga masu saya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa gwamnati ta kafa sabbin hanyoyin sadarwa kamar rediyon manoma da sabis na e-extension, domin bai wa manoma damar samun taimako kai tsaye daga masana.

Ƙarfafa matasa da kirkira.

Kafin isowar Mataimakin Shugaban Ƙasa, za a gudanar da bikin kammala karatun ɗaliban farko na Dikko Social Innovation Academy; wani shiri da ke horar da matasa wajen ƙirƙirar mafita ga matsalolin al’umma.

A cewar Hajiya Malumfashi, ɗaliban sun ƙirƙiri muhimman ayyuka kamar sarrafar shara zuwa kayan gini da canja ragowar amfanin gona zuwa makamashi.

“Waɗannan matasan masu ƙirƙira suna gina makomar Katsina daga ra’ayi ɗaya zuwa na gaba,” in ji ta.

Amincewar Gwamnatin Tarayya da nasarorin Gwamnan Jihar.

A yayin taron manema labaran, dukkan kwamishinonin sun jaddada cewa ziyarar Mataimakin Shugaban Ƙasa na nuna amincewar Gwamnatin Tarayya da nasarorin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Radda ke jan ragamarsu wajen sauya jihar zuwa cibiyar ci gaban tattalin arziki mai dogaro da fasaha da kuma ƙirƙira irin ta zamani, suna masu bayyana cewar duk wani shiri daga MSME Clinic zuwa KASPA yana nufin inganta rayuwar talakawa, wanda sakamakon hakan duka daga hangen nesa ne na gwamna Radda don burinsa na canza dama zuwa arziki ga al’ummar jihar.

Follow Us