Fulani masu dauke makamai sun kai hari kankia ...sun kashe mutum daya sun kwashi dabbobi

Daga Rahoton daily trust @ katsina times Jaridar daily trust ta yau laraba ta ruwaito cewa fulani dauke da makamai sun kai....

Katsina City News October 15, 2025  ·  12:00 AM
| 1,127 Views

Daga Rahoton daily trust 
@ katsina times 

Jaridar daily trust ta yau laraba ta ruwaito cewa fulani dauke da makamai sun kai hari kauyuka da yawa a karamar hukumar kankia ta jahar katsina.

Jaridar tace harin ya faru ne a daren ranar litinin data gabata a garuruwan kwadawa dake Gachi da Bogga,Taiba Badole ,Arahiya kwadawa,Rumawa,Sugar Bindo  fakuwa/ kahin dangi.

Jaridar tace Maharan sun kai su dari a bisa babura.

Jaridar tace, mazauna yankin kankia da kusada sun lura cewa tun bayan zaman lafiya da akace anyi a yankin funtua ake ganin fuskokin wasu bakin fulani a yankin.

Jaridar tace rundunar yan sanda sun tabbatar da harin kuma suna daukar mataki akai,

Advertisement

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 1 + 6?