GWAMNA DAUDA LAWAL YA ƘADDAMAR DA SHIRIN TSAFTACE MUHALLI NA ZAYOSAP
- Super Admin
- 12 Aug, 2023
- 431
Gwamna Dauda Lawal, a ranar Juma’a, ya ƙaddamar da Shirin tsaftace muhalli na ‘Zamfara Youth Sanitation Programme’ (ZAYOSAP) domin tsaftace babban birnin Jihar Zamfara da kewaye.
Gwamnan, a yayin bikin ƙaddamar da shirin a tsohon ɗakin taro na gidan gwamnati da ke Gusau, ya jaddada cewa shirin yana daga cikin shirye-shiryen da gwamnatinsa ta ke da su domin tsaftar muhalli da kiyaye yaɗuwar cututtuka.
Wata sanarwar manema labarai da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce wannan shiri na tsaftace muhalli an ƙirƙire shi ne domin samar da ayyukan yi ga matasa a faɗin jihar.
Ya ƙara da cewa, sashe na farko na shirin ya fara ne da mutum 1, 500, waɗanda aka zaɓo daga gundumomi biyar na ƙaramar hukumar Gusau.
Haka nan kuma shirin yana da ko’odineta 10 da masu bibiya 65. Matasa 1, 500 ɗin an zaɓo su ne daga gudumomin Galadima, Mayana, Madawaki, Sabon Gari da Tudun Wada.
A jawabinsa, Gwamna Dauda Lawal ya buƙaci waɗannan matasa da su jajirce a aikinsu, su kuma mai da hankali kan nauyin da aka ɗaura musu.
Ya ce: “Gwamnatin Jihar Zamfara tana cike da damuwa matuƙa kan makomar matasa, a dalilin haka ne ta ke ta lalubo hanyoyi don yin abubuwan da za su maida matasan masu amfani ga al’umma.
“Baya ga samar da ayyukan yi ga matasa, wannan shiri na ZAYOSAP zai taimaka wurin tsaftace muhalli, ya kuma kare yaɗuwar cututtuka. Tsaftace muhalli yana daga cikin shirin gwamnatinmu na gina birane.
“Don samar da ƙarin ayyuka, mun cimma matsaya da kamfanin da aka ba kwangilar yin tituna a Gusau cewa zai ɗauki matasa 200 domin gudanar da wannan aiki. Haka kuma zamu faɗaɗa wannan aiki zuwa sauran ƙananan hukumomi.” In ji shi.
A yayin da yake jawabi, Ɗan Majalisa mai wakiltar Gusau da Tsafe, Honorabul Kabiru Amadu Mai Palace ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin jihar bisa wannan shiri, inda ya ce, ya zo a daidai lokacin da ake buƙatarsa.
Shi ma Ko’odinetan shirin na ZAYOSAP, Kabiru Muhammad Danyadado ya gode wa gwamnan bisa cika alƙawarin da ya yi wa matasa a lokacin kamfen.