Sulhu da ’yan bindiga: Darasi daga tsagerun Neja-Delta ...Daga bakunan ganau

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes29092025_180230_FB_IMG_1759168768574.jpg

Daga Danjuma Katsina 
@katsina times 


Yankin Neja-Delta nan ne yankin da ake hako albarkatun man fetur a Najeriya. Shi ne yankin da ke rike da tattalin arzikin Najeriya.

Yanki ne da suka dade suna fafutukar neman ’yancin kai zuwa neman damar a ba su cikakkiyar damar amfani da arzikin su.

Wanda ya fara daukar makami a yankin shi ne Adam Adaka Boro. Ya hada runduna a shekarar 1966, ya fara kai wa jami’an Najeriya hari ranar 13 ga Fabrairu, 1966 da shelanta ’yancin kasarsu. Sojan Najeriya sun murkushe shi bayan yakin da aka kira na kwana sha biyu. An yi masa afuwa, har ya taimaka ma Najeriya a yakin da ta yi da kasar biyafara, kuma ya mutu a 1968.

Wanda ya fara yekuwar neman a ba yankin damar amfani da albarkatun kasar su, amma ta fafutukar da ba ruwan ta da makami shi ne Ken Saro Wiwa da kungiyarsa mai suna MOSSOP, wani shahararen marubucin zube da wasan kwaikwayo da kuma wasan kwaikwayo na talabijin. 

Ya yi fafuta mai neman a ba yankinsu na Ogoni ’yancin cin gashin kai da damar sarrafa albarkatun da ke yankinsu da neman kamfanin Shell ya biya al’ummarsa diyya.

Na (marubucin nan) san Ken Saro Wiwa, na halarci jawabansa a Abuja, Kaduna da Legas; a nan muka san juna.

A shekarar 1995 cikin watan Nawumba, shugaban kasa Abaca ya sanya aka rataye shi bisa zargin da hannunsa aka kashe wasu ’yan kabilarsa da basu yarda da ra’ayi irin nasa ba.
Kashe Ken Saro Wiwa ya jawo ma kasar nan koma bayan da har yanzu ba ta dawo daidai ba, domin kasashen Turai sun janye tallafi daban-daban ga Najeriya da har yanzu ba a dawo da su ba.

Hujjarsu, gwagwarmayar Saro Wiwa ba ta makami bace, kuma Abaca yana son kulle bakin duk ’yan adawa ne.

Wanda ya fara daukar makami a tsari irin na ’yan tawaye sosai shi ne Dakubo Asari, wani musulmi dan kabilar Ijaw da ya samo horon sa daga kasar Libya wajen Mu’ammar Ghaddafi.
Dakubo Asari sai da ya tara runduna da kudi sannan ya fara kai harin da ya girgiza kasar nan. Harin ya kai ga wasu jiragen yakin soja, da wasu bututun mai a shekarar 2004.

Dakubo ya ci gaba da kai hare-hare babu kakkautawa. Daga nan ya gayyaci ’yan jaridu. Ina cikin wadanda muka je sansanin sa.

Daga motar da ta kai mu gindin ruwa, an dauke mu a wani karamin jirgin ruwa mai gudun tsiya. Wasu zaratan matasa dauke da makamai suka sa mu tsakiya da kulle mana idanu da wani jan kyalle.

Mun yi ta yawo a ruwa, daga baya aka ce mu bude idanunmu, mu sauka. Rukukin daji ne da ke tsakiyar ruwa, muka yi ta shiga. Daga nan muka isa inda ya yake.

Mun iske yana sallah. Bayan gama sallah, ya yi ma mutanensa jawabin karfafa gwiwa. Sai ya dawo kan mu, ya fada mana dalilinsa na yin abin da yake yi.

A lokacin, a sojojin nasa ba dan kabilar da babu. Har da wani Bahaushe dan Katsina. Ya ce, yana ciki ne a matsayin sojan haya da samun aikin yi. A lokacin 2004, ya ce ana biyan sa dubu dari biyu a wata.

A rahotonmu ne muka ba da shawarar a tattauna da Dakubo Asari, daga abin da muka gani da kuma kalaman bakin sa.

Gwamnatin Obasanjo ta nemi sulhu kai tsaye da Dakubo, inda ta gayyace shi har fadar Shugaban kasa. Ya ba da sharadi. Daga cikin sharadin shi ne zai zo fadar da makaman sa da kuma mutanensa.

Haka aka yi, suka shigo fadar Shugaban kasa cikin jigidar yaki da makamansu a hannu. Shugaban kasa ya yi ma Dakubo tarya ta karimci. Wannan ziyarar an kai ta ne ranar 13 ga Oktoban 2004.

Wannan zaman ya sa aka samu sauki a yankin. Kodayake sun yi wasu ayyukan da suka raunana karfin Dakubo, har aka kama shi, aka tsare shi tsawon lokaci. Daga baya aka sake shi.

Bayan an sake shi da wasu watanni, mun gana da Dakubo a gidansa da ke Abuja. Mutum ne mai addini da kyawawan dabi'un Musulunci. Yanzu haka Dakubo na can garinsu zaune. Shi ne kamar Hakimin garin.

Ƙungiyar da ta yi suna gab da Obasanjo zai bar mulki ita ce MEND, mai suna kungiyar fafutukar 'yantar da Neja-Delta. Suna da shugabannin daban-daban, amma wanda ya yi suna shi ne Tampolo.

Mend kungiya ce da ta hada duk kungiyoyin da ke fafutukar 'yancin Neja-Dalta. Tana da kwamitin amintattu wadanda suka hada har da Dakubo Asari da Tampolo, da Henry Okah. Har yanzu wannan kungiya kansu hade yake, suna magana da gwamnati a daidaiku da kuma da murya daya, musamman suka ga za a cutar da dayansu ko kungiyar sa.

Bayan wasu ayyukan soja da suka girgiza kungiyar, sai gwamnatin Tarayya ta ba da kofar tattaunawa. Wani dan jarida daga jaridun Daily Trust ya samu ganawa da Tampolo, ana tsakiyar wannan gumurzun. Ya kuma rubuta rahoton sa a jaridar waccan lokacin.

Wani dan Katsina wanda ba zan bayyana sunan sa ba, don ban nemi iznin sa ba. Yana aiki a matatar mai ta Bayelsa, yana rike da wani babban mukami, ya taka rawa babba wajen daidai ta kungiyar Mend ta hannun Tampolo da gwamnatin 'Yar'adua a shekarar 2009.

Ya ba ni labari dalla dalla kan me ya faru da yadda aka yi nasara. Har yanzu suna mutunci da Tampolo.

Ana fara tattaunawa, gwamnatin 'Yar'adua ta kawo karshen hare-haren 'yan Mend ga jami'an Najeriya da kaddarorin manta.

Tampolo da yaransa, sune yanzu masu kwangilar kare bututan mai na gwamnatin Tarayya. Sune kuma ke yaki da fitar da mai ta barauniyar hanya. Duk inda zaya akalla jami'an tsaron Najeriya da nasa sun kai hamsin masu tsaron sa.

FULANI MASU RIKE DA MAKAMAI DA TSAGERUN NEJA-DELTA

Daga abin da na sani tsagerun Neja-Dalta, kusan kashi mafi yawansu suna da ilmin boko da addinin da suka yi imani da shi.

Suna da wata manufa da kudirin da suke son cimmawa - shi ne su ke da arziki, amma an bar su a baya, ba su cin gajiyar arzikin.

Ba ruwansu da wanda bai ji, bai gani ba. Ba ruwansu da mutanen gari, sai wanda ya taba su. Jami'an tsaro da kaddarorin gwamnati ne kawai target din su.

Fulanin daji da ke dauke da makami kuwa, sun mayar da lamarinsu a dauki mutane ko a dauki mutum don a kawo kudin fansa. Talakkawa sune suka fi shan wahalarsu. Sun mai da lamarinsu kabilanci.

Bahaushe dole ya kaskanta a gun su. Sun mai da lamarin kamar daukar fansa. An yi mana kaza, sai mun rama. 

A Katsina, lokacin gwamnatin Masari sai da aka cika masu kusan kashin 95 cikin dari na bukatunsu. Aka rusa banga, aka saki 'yan'uwansu daga gidan yari. Masari ya dage aka bar kai masu hari ta sama da kasa, jihar Katsina ta tsaya lafiya lau tsawon kusan shekaru biyu. Gaf da zabe kuma, sai suka koma ruwa.

SULHU DA 'YAN BINDIGA

Sulhun da ake yi a wasu kananan hukumomin yana iya daukar lokaci, a wasu kuma sayen lokaci ne.
Amma idan mutane za su dau matakin kare kansu, kuma jami'an tsaronmu za su yi aiki tsakani da Allah, ana iya samun sulhu ingantacce, mai dorewa

Danjumakatsina. Shine mawallafin jaridunkatsinatimes, katsinacitynews da jaridar taskarlabarai. 07043777779

Follow Us