SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!.
- Katsina City News
- 24 Sep, 2023
- 770
Sashen kula da Samar da ayyukan yi na Jihar Katsina, Watau "Department of Employment Promotion".
Na sanar da 'yan asalin Jihar Katsina, musam man masu sha'awar fadada karatu a bangaren kimiyyar sarrafa tama da karafa wato iron and steel.
Da bangaren sarrafawa da tacewar mai, watau oil and Gas da sauran kwasa- kwasai masu alaqa da masana'antu cewa, Cibiyar nazarin Sarrafa karafa.
Watau "Metallurgical Training Institute Onitsha dake a Jihar Anambra wadda ke karkashin Ma'aikatar Tama da karafa ta tarayya tana gudananar da kwasa-kwasan Diploma a fannoni kamar haka:
(1) Fanni na farko Diploma ta shekara 2 a fannin :
a.Electrical and electronic engineering Technology.
b.Welding and fabrication engineering Technology.
c. Mechanical engineering Technology.
d. Metallurgy and materials Technology
e. Computer Engineering
f.Computer Science Technology
(2) Sai kuma fanni na 2 Diploma ta shekara 3 wadda sama kashi 70 cikin dari ake horaswa a aikace, watau practical, kashi 30 kadai ne a Aji a wadannan Fannoni kamar haka:
i. Industrial Electrical engineering
ii. Instrumentation and control system engineering
iii. Mechanical maintenance engineering
iv. Heavy mobile equipment maintenance engineering
V. Steel fabrication and welding engineering
Vi. industrial Metallurgy and foundry Engineering.
Domin samun gurbin karatu a wannan cibiyar karatu, ana bukatar Dalibi ya cika wadannan sharrudda kamar haka:
I. Dolene Dalibi ya wuce shekuru 16 da haihuwa
ii. kananan hotuna fasfo guda 4 da kuma kudin fom #5,000 kachal wadda ake biya ta hanyar Remita.
iii. Dolene Dalibi yazama yanada akalla Credit 5 a takardun sa na kammala sakandire wanda ya kumshi: Turanci da lissafi da Physics da kuma Chemistry a jarrabawar Neco ko GCE.
iv. Daliban da suke da sakamakon WAEC Technical ko NABTEB ko NTC suma zasu iya nema.
Bugu da kari, ana Sanar da Daliban cewa, Dukannin kwasa-kwasan da ake gudanarwa a wannan Cibiyar na bangaren kere-kere ne,watau Engineering.
Sannan sakamakon da ake bayarwa ga wadan da su ka samu nasarar kammalawa shi ne na "National Diploma".
Saboda haka, ake sanar da wadanda su ka nuna sha'awar shiga wannan makaranta da su tuntubi kananan hukumominsu domin su mika takardun bayanansu kafin nan da ranar Juma'a 3 ga watan Octoba, na shekara ta 2023, da muke ciki.
Sannan akwai Jarrabawar tantancewa ga daliban da suka nuna sha'awar neman gurbin karatu a makarantar a ranar Asabar 14 ga watan October a mazaunin makarantar na din-din- din dake a Onitsha Jihar Anambra.
Domin neman karin bayani, sai a ziyarci babbar hedikwatar Sashen samar da aikin yi ta Jihar Katsina da ke a bayan gidan Labo Tarka a GRA cikin garin Katsina
Sanarwa daga: Rilwanu Muhammad Batagarawa a madadin Mai baiwa Gwamna shawara akan samar da ayyukan yi.