Jonathan Ya Ziyarci Shugaban ADC, David Mark – Ana Hasashen 2027

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes26092025_160109_c04f3490-7203-11f0-b21f-5bdb6d834b46.jpg.webp



Katsina Times 

Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya kai ziyarar ban-girma ga shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), David Mark, a daren Alhamis a birnin Abuja.

Ziyarar ta zo ne bayan jam’iyyar ADC ta gudanar da taron kwamitin riko na ƙasa karo na farko tun bayan da aka amince da jam’iyyar a matsayin dandalin haɗin kan siyasa. Wannan mataki ya sake tayar da jita-jitar makomar siyasar Jonathan, musamman dangane da zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A cikin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar na ci gaba da tattaunawa da Jonathan domin ya sake shiga takara da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, muddin Tinubu ya samu tikitin jam’iyyar APC a 2025.

Jonathan, wanda ya shugabanci Najeriya har zuwa faduwarsa a hannun marigayi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a 2015, doka ta ba shi damar yin wa’adi guda tilo idan ya tsaya takara kuma ya ci.

Duk da cewa ba a bayyana ainihin dalilin ganawar ba, Jonathan da Mark suna da dogon tarihin siyasa tare. A lokacin da Mark ke shugabantar Majalisar Dattawa, ne aka aiwatar da Doktrinin Bukata (Doctrine of Necessity) wanda ya bai wa Jonathan damar zama shugaban ƙasa na rikon kwarya a lokacin da marigayi shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua ya yi doguwar rashin lafiya.

Follow Us