Abubakar Gege ya zama sabon shugaban Kungiyar UDYF
- Katsina City News
- 23 Sep, 2023
- 847
Alh Abubakar Gege ya zama sabon shugaban kungiyar Unguwar Yari Development Forum (UDYF)
Daga Shafin Mobile Media Crew
Ranar asabar 23-09-2023 al'ummar unguwar suka fito domin kada kuri'arsu a harabar sakatariyar karamar hukumar Katsina. Hon Kamal Mamman unguwar Yari shugaban majalisar kansiloli na karamar hukumar Katsina na daya daga cikin wadanda suka kada kuri'arsu.
Zaben anyi shi lafiya an gama lafiya, ba tare da wata hayaniya ba.