
Daga:- Muhammad Ali Hafizy. | Katsina Times.
A wannan shekarar ta 1447, (Bayan hijira) Kungiyar Munazzamatu Fitiyanil Islam ta kasa reshen jihar Katsina, tare da majalissar shura ta malaman zaure na jihar Katsina, sun gudanar da mauludin Manzon Allah (S,A,W) a karamar hukumar Bindawa ta jihar Katsina kamar yadda suka saba a kowace shekara.
A duk shekara kungiyar tana zabar wata karamar hukuma sai tayi mauludin a can, a bisa tsarin shiyoyin da muke da su a jihar Katsina wanda ya haɗa da shiryar Katsina, shiryar Daura, da shiryar Funtua. To a bana an zabi shiyar Daura, a karamar hukumar Bindawa aka gudanar da mauludin a can, a ranar Asabar 20 ga watan Satumba 2025.
Taron mauludin na bana ya tattaro abubuwa da yawa, wadanda aka ja hankalin mahalarta taron dasu, musamman gyaran tarbiyyar al'umma da kuma kiyaye yin maganganu wadanda basu kama, ta ba ga janibin Manzon Allah (S,AW,), da kuma muhimmantar da addu'o'in zaman lafiya a jihar Katsina da ma kasa baki ɗaya.
Haka zalika taron ya samu halartar manyan malamai, almajirai, shugabannin kungiyar a matakin kasa, yan uwa da abokan arziki, yan siyasa da kuma masu ruwa da tsaki a harkokin addini. Ya kuma samu halartar Kwamishinan addinai na jihar, sakataren gwamnatin jihar Katsina Alhaji Abdullahi Garba Faskari, Shugaban Mu'assatul Khairiyya Hajiya Hauwa Radda da dai sauransu.