Tsohon Dogarin Gwamna Masari ya raba Tallafin Masara ga Mata 2000 a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes20092025_192937_FB_IMG_1758396530008.jpg

Katsina Times 


A ranar Asabar 20 ga watan Satumba 2025 Tsohon Dogarin tsohon gwamnan jihar Katsina Aminu Masari, Lawal Ahmad Joka ya raba Tallafin masara da kudin abin hawa ga mata dubu biyu a karamar hukumar Katsina.

Da yake jawabi a wajen bada tallafin abinci Joka ya bayyana cewa ya bada wannan tallafi ne albarkacin watan maulidin Annabi (S), yace duba da mata iyaye suna hidima sosai sama kuma akwai gagarumin zagayen maulidin a gaban mu, ya dace mu taimaka wa matan don su yi abinci da zai rage masu wata hidimar.

Joka ya bayyana cewa wannan mata ne kawai zasu amfani wannan tallafi na abinci inda aka tantance mace dubu biyu, yace zuwa nan ba da jimawa ba suma maza na karamar hukumar Katsina za a duba mabukata don tallafa masu.

Alhaji Tanimu Sada tsohon mai taimakawa Gwamna Masari ya halarci wajen taron da aka gudanar a gidan Joka dake unguwar kwado daura da hamada carpet cikin Katsina, inda ya bayyana cewa hidimar dama ba yau aka saba ba, yace mun yi, kuma muna iya karfin mu don tallafawa masu bukata, haka zalika tun  da watan maulidin Annabi (S) ya tsaya muka zabi tallafawa wajen maulidi a aljihu, jiki da aiki don yin musharaka a cikin ladar.

Shima shugaban Kansilolin karamar hukumar Katsina da ya wakilci shugaban karamar hukumar Katsina, ya yaba da wannan kwazo na Joka inda ya isar da sakon isa Miqdad Shugaban karamar hukumar Katsina gami da bada uzurin sa na rashin halartar taron.

Yayi fatan alheri tare da ƙara jinjina wa Lawal Ahmad Joka bisa wannan kokari duk da bashi rike da wani mukami a gwamnati.

Taron ya samu halartar Dattawa, Yan siyasa, Kansilolin karamar hukumar da sauran al'umma.

Follow Us